Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata

Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata

- Shuganan bankin AfDB Akinwumi Adesina ya kare Yakubu Gowon kan zargin da wani dan majalisar dokokin Birtaniya yayi a kansa

- Dan majalisar ya zargi tsohon shugaban kasar a mulkin soja da sace rabin kudin CBN a lokacin da aka yi masa juyin mulki

- Sai dai Adesina, ya yi watsi da zargin, yace Gowon mutum ne mai mutunci da gaskiya

Akinwumi Adesina, Shugaban bankin ci gaban Afrika (AfDB), ya yi martani a kan ikirarin wani dan majalisar Birtanita, Tom Tugendhat, cewa Yakubu Gowon ya sace rabin kudin babban bankin Najeriya a lokacin da aka yi masa juyin mulki a 1975.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin kudu maso kudu sun gabatar da wasu manyan bukatu 5 a gaban Buhari

Tugendhat, wani dan majalisar Birtaniya, ne yayi zargin a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, lokacin da suke mahawara a kan kira ga hukunta jami’an gwamnatin Najeriya kan cin zarafin mutane a zanga-zangar #EndSARS.

Sai dai, a wani wallafa da yayi a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, Adesina wanda ya kasance tsohon ministan noma na Najeriya, ya bayyana zargin a matsayin batarwa.

Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata
Mutum ne mai mutunci, Shugaban bankin AfDB Adesina ya kare Gowon kan zargin sata Hoto: Twitter/@akin_adesina, Stephen Kelly/Getty Images
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro shugaban na AfDB ya ce, Gowon wanda ya kasance tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja ya kasance dattijo abun sha’awa mai gaskiya da mutunci.

Ya wallafa a shafin nasa:

“Ku yi hankali da bayanan batarwa! Mai girma Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya kasance mutum mai martaba sosai, kamili, gaskiya, saukin kai, karamci da mutunci. Na san shi. Dattijon Najeriya abun sha’awa. Gaskiyarsa da mutuncinsa na da tasiri."

KU KARANTA KUMA: Gwamna ya umarci kwamishinansa da ya tafi jinyar tsohon shugaban majalisar dattawa a Landan

A baya mun ji cewa Gowon ya mayar da martani ga dan majalisar dokokin Birtaniya wanda ya zarge shi da sace rabin kudin CBN a 1975.

Tsohon shugaban kasar a mulkin soja ya karyata zargin, inda ya bayyana shi a matsayin “shirme” kuma ba gaskiya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel