Hukumar kurkukun Kuje ta saka takunkumi, ta hana 'yan majalisa ganin Ndume
- An hana wasu sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran halin Kuje da ke Abuja
- An garkame Ndume ne a maimakon Maina, tsohon shugaban hukumar fansho
- Sanata Na'Allah da yaje ganinsa ya ce bai taba ganin irin wannan wulakancin ba
An hana sanatoci damar ganin Ndume a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja. An garkame shi a ranar Litinin saboda rashin samun damar bayyana tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa.
Alkali Okon Abang na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya umarci a damke Ndume bayan wanda ya tsaya wa ya kasa bayyana a kotu a kan zargin satar naira biliyan 2 na kudin fansho, Daily Trust ta ce.
Masu rajin kare hakkin bil'adama suna bukatar a saki Ndume iya wuya. Duk da bayanai sun kammala a kan yadda aka ga sanatoci suna kai-kawo a gidan gyaran hali don ganin Ndume a ranar Talata.
KU KARANTA: 2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki
Sanata Ishaku Elisha Abbo, sanatan PDP na Adamawa, inda aka ji yana ce wa Sanata Bala Ibn Na'Allah, na APC jihar Kebbi, sai ya tambayi ma'aikatan gidan gyaran hali amma sam sun hana shi ganinsa.
Sai da sanata Na'Allah suka tattauna da Abbo tukunna aka basu damar shiga wani ofishi. An ga sanatan ya shiga ofishin wani babban jami'i, G. U. Ochepa, bayan ya cika dokokin kariya daga COVID-19.
An ji Ochepa yana ce wa sanatan: "An hana ziyara saboda COVID-19. Ba horo ne ga sanatan ba."
Lauyansa da matansa ne kadai za su samu damar ganinsa. Bayan ya yi mintoci 20 a ofishin Ochepa, sanatan ya bar gidan gyaran halin. Na'Allah ya nuna tsananin tsoron da ya shiga a kan damkar Ndume da aka yi.
"Tsawon shekaru na a matsayina na lauya, wannan ne karo na farko da naga irin wannan wulakancin. Nasan indai har tsayayye ya kasa bayyanar da wanda ya tsaya ma wa, kudi zai biya na beli.
"Kudin belin ne yakamata ya biya, amma ban taba ganin an garkame tsayayye ba a maimakon wanda ya tsaya wa," a cewarsa.
KU KARANTA: Hotunan budurwa mai shekaru 19 ta banka wa gidan tsohon saurayi wuta, ta kone sabuwar budurwarsa
A jiya mun ji cewa Sanata Ali Ndume, wanda ma'aikatan gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, suka tafi da shi a ranar Litinin, a bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja, zai daukaka kara akan hukunci da aka masa yau, Talata.
Lauyan Ndume, Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, Daily Trust ta tabbatar.
A cewarsa, ba a ba iwa Ndume damar jin ta bakinsa ba, sannan ba su bashi wasu takardu da ya bukata ba don ya kare kansa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng