Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

- Iyalan mai tallar jaridar da mai tsaron kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya kashe sun nemi kudin fansa

- Iyalan sun nemi shugaban majalisar ya biya su kudi Naira miliyan 500 duba da cewa ya kashe mai ciyar da gidansu

- A makon daya gabata ne wani cikin masu tsaron Gbajabiamila ya harbe mai tallar jarida amma yanzu yana tsare

Iyalan Ifeanyi Okereke, wani mai siyar da jarida da mai tsaron lafiyar Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya bindige har lahira sun bukaci naira miliyan 500 daga gare shi.

Satin da ya gabata, wani jami'in hukumar tsaron farin kaya (DSS) Abdullahi Hassan da ke tsaron shugaban majalisar, ya harbe Okereke.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, bukatar na kunshe ne a cikin wata takarda da lauyan iyalan Mike Ozekhome ya aikewa Femi.

Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira dubu 500 daga kakakin majalisa
Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira dubu 500 daga kakakin majalisa. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

A wasikar mai dauke da kwanan wata 23 ga Nuwamba, iyalan Okereke sun ce abun da suka nema ba zai iya maye gurbin dansu ba.

"Wanda muke karewa sun umarci da mu nemar musu wadannan hakkoki daga wajen ku:

Kayi amfani da matsayin ka wajen ganin an gurfanar da jami'in tsaron ka (Abdullahi Hassan), wanda saboda jin dadi, ya fita daga hurumin aikin sa ya kuma harbe mutumin da bai ji ba bai gani ba," a cewar Ozekhome.

DUBA WANNAN: Gandirebobi da 'yan acaba sunyi rikici a Agodi

"Kuma ka biya iyalan Okereke Naira miliyan 500 kacal.

"Biyan wannan kudi baza su iya maye gurbin sa a matsayin ɗa, miji, da kuma dan uwa ba. Amma hakan zai rage bakin ciki da kuma radadin da kunchin rayuwa da mutuwar ta sa su."

Kuma lauyan ya bayyana idan aka gaza biyan bukatun cikin sati guda, za su dauki mataki na shari'a.

"A kuma lura cewa wannan bukatun wadda muke karewa ne, idan aka ki bi ko a banzatar da bukatar cikin mako guda daga kwanan watan da ke jikin wasikar, zamu dauki matakin da ya dace na shari'a, don bi wa wanda muke karewa hakki", a cewar sa.

Gbajabiamila ya ce ya mika jami'in gaban rundunar DSS don hukunta shi.

Ya kuma ziyarci iyalan don yi musu ta'aziyya.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel