Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP

Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP

- Gwamna Bala Mohammad na Jihar Bauchi ya musanta raɗe raɗin cewa zai fice daga jam'iyyar PDP

- Gwamnan ya bayyana cewa duk wani batu dangane da canjin sheka ko zaɓen 2023 abu ne da zai kawo tsaiko wajen cika alkawarin da ya dauka lokacin yaƙin neman zabe

- Ya shawarci jama'a suyi watsi da rahoton tare da jaddada aniyarsa na inganta rayuwar al'ummar Bauchi ba tare da nuna bambanci ba

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP
Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP. Hoto daga @channelstv
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

"Muna so mu sanar cewa wannan labarin karya ne da aka kirkira saboda wata bukata ta kashin kai, don jawo hankali masu bibiyar labaran siyasa wanda ficewar gwamnan Ebonyi ya sake ta'azzara labarin siyasar ƙasar," a cewar Gidado.

Ya ƙara da cewa, "muna su mu sanar da cewa mai girma Gwamna Sanata Bala Mohammad bai taɓa kokonton barin PDP zuwa APC ba.

"Sai dai, yanzu yana tsaka da cika alkawuran da ya ɗauka lokacin yakin neman zaɓe, wanda akan haka al'ummar Bauchi suka goya masa baya ya kifar da gwamnati mai ci."

KU KARANTA: 'Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Don haka, Gwamna Bala Mohammed yana ɗaukar magana akan canja jam'iyya da zance akan 2023 a matsayin abin da zai ɗauke masa hankali," kamar yadda Gidado ya bayyana.

Saboda haka, gwamnan yana shawartar masoyansa sa, ƴan jam'iyyar PDP da al'ummar Bauchi da suyi watsi da rahoton.

Ya kuma jaddada aniyarsa na inganta rayuwar al'umma mazauna Bauchi ba tare da nuna bambanci ba.

A wani labarin, an kama wata mata mai shekaru 40 da haihuwa mai suna Ruqayya Rabi'u a Jigawa bayan samun ta da jabun kuɗade (dubu ɗai-dai guda 100 da ɗari biyar-biyar guda 76) a ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Wacce ake zargin dai ƴar asalin ƙaramar hukumar Bichi ne a Kano ta shiga hannu ne bayan ta siya man shafawa na N300 a kasuwa kamar yadda LIB ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel