Gandirebobi da 'yan acaba sunyi rikici a Agodi

Gandirebobi da 'yan acaba sunyi rikici a Agodi

- An tafka mummunan rikici tsakanin 'yan acaba da gandirebobi na gidan yarin Agodi Gate a Oyo

- Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne bayan da gandirebobin suka harbe wasu mutane biyu

- Hakan ya janyo zanga zanga da kone konen tayoyi a kan tituna wadda hakan yasa aka tura jami'an tsaro wurin

Hankula sun tashi a unguwar Agodi Gate bayan rikici da aka yi tsakanin masu sana'ar acaba da ma'aikatan gidan gyaran hali na Agodi da ke Ibadan kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ba a san ainihin abinda ya janyo rikicin da aka fara tun safiyar ranar Talata ba kawo yanzu sai dai The Punch ta ruwaito cewa an ce gandirebobi sun harbe mutane biyu.

Ma'aikatan gidan yari da 'yan acaba sun bawa hammata iska a Ibadan
Ma'aikatan gidan yari da 'yan acaba sun bawa hammata iska a Ibadan. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Makanikai biyu da suka tafi kasuwar sayar da kayan motocci da ke kusa da gidan gyaran halin sun shaidawa wakilin majiyar Legit.ng cewa a fuska aka harbi daya daga cikin mutanen da abin ya faru da su.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara

Daya daga cikin mutanen da ya ce sunansa Taye Odewale, ya ce ba zai iya tabbatarwa ba ko wanda aka harba dan acaba ne, dan kasuwa ko kuma wucewa kawai mutumin ke yi.

Wani mutum da ke sayar da abin sha a unguwar ya tabbatar da rikicin ya ce matasa sun kunna wuta a kan tituna suna zanga zanga game da kashe mutanen.

Kakakin 'yan sandan Jihar Oyo, Mista Olugbenga Fadeyi, da aka tuntube shi ya ce an tura 'yan sanda da wasu jami'an tsaro wurin don hana 'yan daba kai hari gidan yarin.

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Kakakin 'yan sandan ya ce, "Ba gaskiya bane cewa 'yan sanda ne suka yi harbi da ya janyo rikici a Agodi gate kamar yadda wasu ke yadawa a intanet.

"Gaskiyar abinda ta faru shine an samu rikici tsakanin gandirebobi na gidan yarin da masu acaba a Agodi Gate.

"Bayan samun rahoton, an tura 'yan sanda da wasu jami'an tsaro wurin don tabbatar da cewa an dakile rikicin kada ya kai ga hari a gidan gyaran halin."

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel