Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban

Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban

- Wani dan sanda ya harbi wani saurayi a harabar Otal din Ekiti, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa

- Kamar yadda gidan talabijin na Channels suka tabbatar, al'amarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020

- Bayan kashe saurayin, dan sandan ya dauke gawar ya yaddar a asibitin koyarwa na jihar Ekiti, ya tsere

Wani dan sanda ya harbi wani saurayi mai suna Olaoye Akintayo, a ranar 21 ga watan Nuwamban 2020, inda take a nan ya rasa ransa. Saurayin ya raka abokansa otal din Ekiti ne, kamar yadda gidan talabijin din Channels suka tabbatar.

Kisan da 'yan sanda suke yi ba tare da kotu ta bayar da izini ba ya kara yawaita ne tun bayan zanga-zangar EndSARS, wanda aka yi don dakatar da cin zarafin da 'yan sanda suke yi.

Kamar yadda abokan mamacin da wasu ganau suka tabbatar, dan sandan ya shigo harabar Otal din cikin wata mota, kirar Hilux, sai dai suka ji karar harbi.

Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban
Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban. Hoto daga @Channelstv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa

Ba a san abinda ya janyo harbe-harben ba, wanda yayi sanadiyyar raunata wani daban.

Dan sandan da abokan aikinsa sun dauki gawar saurayin, inda suka jefar da shi a harabar asibitin koyarwa na jihar Ekiti, daga nan suka ajiye motar a harabar asibitin, suka tsere.

Jami'in hulda da jama'an jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar wa da gidan talabijin din Channels cewa an damki dan sandan, duk da dai har yanzu ba a riga an gano dalilin harbin ba.

Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban
Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban. Hoto daga @ChannelTv
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa

A wani labari na daban, an tsinci gawar shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi. Wata majiya da take kusa da iyalan mutumin ne ta sanar da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi da rana.

Sannan wani shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar. Duk da dai har yanzu jam'iyyar APC ba ta riga ta yi magana ba a kan garkuwa da shi da aka yi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel