Da duminsa: An tsinci gawar shugaban APC da aka sace a daren Asabar
- An tsinci gawar shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa
- Wata majiya ta kusa da iyalansu, ta shaida wa manema labarai hakan a ranar Lahadi
- Duk da dai har yanzu jam'iyyar APC bata riga ta ce komai ba a kan lamarin
An tsinci gawar shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi.
Wata majiya da take kusa da iyalan mutumin ne ta sanar da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi da rana.
Sannan wani shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar.
Duk da dai har yanzu jam'iyyar APC ba ta riga ta yi magana ba a kan garkuwa da shi da aka yi ba.
Shugaban karamar hukumar Karu, Samuel Akala, ya tabbatar da mutuwar a shafinsa na sada zumuntar zamani ta Facebook.
Dama PREMIUM TIMES ta sanar da garkuwa da Shekwa da aka yi a ranar Asabar a gidansa da yake Lafia.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Nasarawa, Dele Longe, ya tabbatar da garkuwa da shi da aka yi da safiyar Lahadi.
KU KARANTA: Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima
KU KARANTA: EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi
Idan za mu tuna, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.
Gidan na kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a Lafia. Sun isa gidan wurin karfe 11 na dare inda suka yi awon gaba da shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng