Gwamnatin tarayya ta kammala shirin zabge harajin motoci da kaso biyar

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin zabge harajin motoci da kaso biyar

- A shekarar 2019 ne shugaban hukumar kwatsan, Hameed Ali, ya shawarci gwamnati ta rage harajin shigo da motoc

- Hameed Ali ya ce kara farashin da gwamnati ta yi ya sace gwuiwar masu sana'ar sayar da motoci tare da kara yawan matsalar fasa kwauri

- Yanzu haka, gwamnati tarayya ta sanar da cewa ta kammala dukkan tsare-tsare domin zabtare harajin motoci

Gwamnatin tarayya ta gama kammala tsare tsare don ganin ta zabge harajin motocin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje daga kaso 35% zuwa kaso 30%.

Wannan na cikin ƙunshin ƙudiran shekarar 2020 da ma'aikatar kuɗi za ta gabatarwa majalisar dattijai, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Ƙudirin zai zamo doka da zarar ƴan majalisu da Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, sun amince da shirin.

KARANTA: Fashola ya bayyana dalilin da yasa ba'a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna da Abuja ba

Bayanan ƙudirin, wanda fadar shugaban ƙasa ta watsa, ya nuna cewar harajin Tan-Tan, manyan motocin dakon kaya, da sauran motocin aikin gona, za'a zabge su daga kaso 35% zuwa kaso 10%.

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin zabge harajin motoci da kaso biyar
Gwamnatin tarayya ta kammala shirin zabge harajin motoci da kaso biyar @Thecable
Asali: Twitter

Tsarin ya ɗauke biyan haraji ga kamfanonin da suka bada gudunmawar tallafin annobar COVID-19 a ƙarƙashin inuwar kamfanoni masu zaman kansu da ke yaƙi da annobar Korona (CACOVID).

Domin rage raɗaɗi da kawo sauƙin kasuwanci, kudirin ya kawo shawara mallakar manhaja a matsayin kuɗaɗen da aka kashe wajen gudanar da kasuwanci.

Zainab Ahmad, ministar kuɗi, kasafi da tsare tsare, a baya baya nan ta yi bayani kan yadda za'a zabge harajin shigo da kayayyaki don ragewa da sauƙaka kuɗin tafiye tafiye.

KARANTA: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ba; jigo a APC, Farfesa Mahuta

"Dalili da manufar yin hakan shine mu rage tsadar kuɗin tafiye tafiye, wanda jigo ne wajen haifar da hauhawar farashin kayayyaki" Zainab ta faɗawa manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan kammala wani taron ƙusoshin gwamnati a ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba.

A shekarar 2019, Hameed Ali, shugaban hukumar Kwastam ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta rage harajin da ake biya akan motocin da ake shigowa dasu zuwa kaso 10%.

A wancan lokacin, Hameed Ali, ya yi gardamar cewa yawan harajin da ake biya ƙari akan kaso 35% ya sacewa masu shigo da motocin guiwa, wanda ya jawo suke shigo da motocin zuwa maƙwabtan ƙasashe domin su yi fasa ƙwaurinsu.

A cikin makon da muka yi bankwana da shi, Legit.ng ta rawato cewa ministar kudi, Zainab Ahmed, ta ce tsadar kudin dako da tafiye-tafiye ke haddasa matsalar hauhawar farashin kayayyaki

Zainab ta ce gwamnati ta bullo da wani tsari da zai ragewa jama'a kudaden da suke kashewa wajen tafiye-tafiye da dakon kayansu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel