Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi

Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi

- Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana cewa laifi daya da ake zarginsa da aikatawa a PDP shine cewa ya ki sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Umahi ya ce wannan dalili ne yasa ake zarginsa da yi wa jam'iyyar adawar kasar zagon kasa ta hanyar fallasa bayananta

- Ya ce ko daya bai yi danasanin barin PDP zuwa APC ba don kwatarwa yankinsa yanci

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, ya ce ya zama abun zargi a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda kawai ya ki caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya yi furucin ne yayinda yake jawabi ga manema labarai a Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi kan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

Gwamna Umahi ya ce: “Kowani mutum na tafiya ne da kaddararsa. Alkawari guda da na dauka shine cewa ba zan taba sukar PDP ba; kamar yadda a lokacin da nake PDP, zunubi na guda shine cewa na ki matsawa Shugaban kasa kuma har abada, ba zan taba yin hakan ba saboda wannan shine halayyar gidan da na fito.

Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi
Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

“Amma wadanda basu da hali, sun kasance masu zargina saboda bana sukar Shugaban kasar, cewa ina iya yiwa PDP zagon kasa ta hanyar fallasa bayananta.

“Wani irin rashin hankali ne wannan? Na fito daga sananen gida inda akwai tarbiya. Don haka, ina da tarbiya; babu wanda zai iya bugun kirji a APC ko PDP cewa duk abunda aka tattauna, zan je na fallasa. Na fallasa shi saboda me? Shin saboda kudi ne, ko kuma saboda suna?” ya tambaya.

Gwamnan ya bayyana cewa bai yi danasanin barin PDP zuwa APC ba domin ya yi zanga zanga a kan abunda ya bayyana a matsayin rashin adalcin da jam’iyyar adawa ke yi wa Kudu maso gabas.

A cewarsa, ikirarin da ake na cewa ya bar PDP saboda son tsayawa takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa ba gaskiya bane.

Gwamna Umahi ya kara da cewa ya yi gayya a matsayin gwamna sau biyu, inda ya kara da cewar zai bar harkar siyasa a 2023, Channels TV ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Atiku Abubakar ya miƙa ƙoƙon bara ga mambobin PDP na shiyyar Kudu kan zaben 2023

Ya bayyana cewa: “A sani cewa babu wanda ya yi mun alkawarin komai, kowa ya kwana da sanin cewa na sauya sheka ne saboda rashin adalci, kuma bana danasani game da hakan.

“Wasu mutane sun ce zan yi danasanin wannan yunkuri, na yi masu dariya; sai kace sun ga Allah, sai kace sune Allah na. Na gamsu da kasancewana dan kasuwa, na gamsu da yin kasuwancina kuma shikenan babu wani abu.”

A wani labarin, kakakin jam'iyyar APC na jihar Ebonyi, Chika Nwoba, ya yi murabus daga kujerarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel