Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)

Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)

- Addinin Musulunci ya samu babban karuwa na wasu fastoci 42 da Bishop biyu

- Fastocin sun karbi musulunci ne tare da iyalansu a babban masallacin kasa da ke Abuja

- An kuma gudanar da wani muhimmin taro domin wayar masu da kai a kan shika-shikan addinin Musulunci

Labari da muke samu sun nuna cewa wasu fastoci 42 da kuma manyan limaman bishop biyu tare da iyalansu sun amshi addinin musulunci.

An yi taron musuluntar da su ne a dakin taro na babban masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja.

An kuma gudanar da taron kara ma juna sani na tsawon kwanaki bakwai domin wayar masu da kai a kan shika-shikan addinin Musulunci.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kai samame maboyar masu laifi, sun kama mutane 720 da makamai a Legas

Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja (hotuna)
Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja Hoto: @AysherSadiq
Asali: Twitter

A wani wallafa da wata mai amfani da shafin Twitter, @AysherSadiq ta yi, an gano hotunan fastocin tare da iyalansu cikin shiga ta mutunci inda mazan suka sanya dogayen rigunan tazarce, matan kuma sun kasance sanye da hijabai.

Aysher ta wallafa a shafin nata cewa: “Fastoci 42, bishops biyu da iyalansu sun amshi addinin Musulunci a dakin taro na babban masallacin kasa, Abuja. An gudanar da taron kwanaki bakwai domin koyar da su shika-shikan Musulunci. Masha Allah."

KU KARANTA KUMA: Zaman ɗari ɗari: Yan sanda sun kashe mutane biyu a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa a kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasarta da zamantakewa, kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa wasu dokokin shari’ar Musuluncin kasar gyaran fuska, inda a yanzu ta halasta shan giya da zaman dadiro.

Wannan kwaskwarima da kasar ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ta ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

A ganin UAE hakan da ta yi zai habbaka tattalin arzikinta tare da nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai sassaucin ra’ayi, karbar sauyi da kuma tafiya da zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng