Hotunan Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce

Hotunan Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce

- Bashir, dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya

- Dan shahararren dan siyasan ya wallafa hotunansa da amaryarsa a shafinsa na Twitter lamarin da sa matasan arewa yamutsa gashin baki

- Da dama sun caccaki ma’auratan inda suka bayyana cewa sam hotunan basu dace ba

Bashir El-Rufai, daya daga cikin yaran gwamnan jihar Kaduna, ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya wallafa hotunansa da amaryarsa a kan Twitter.

A cikin hotunan, an gano Bashir rike da kugun amaryarsa yayinda ita ma ta kamo shi cike da kauna.

KU KARANTA KUMA: Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi

Hotunan bikin Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce
Hotunan bikin Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

A wani hoto kuma, an gano Bashir yana sumbatar amaryarsa a kumatu yayinda ita kuma ta rike fuskarsa tana murmusawa.

Sai dai kuma hakan ya fusata musulmai da Hausawa da ke amfani da Twitter inda suka yi wa hakan kallon bai dace ba.

KU KARANTA KUMA: Rabon kwado: Gwamna Inuwa Yahaya ya ba wanda ya yi wa Buhari tattaki kyautar mota da N2m

Ga wasu daga cikin sharhin mabiyansa:

@AbdulMalumfash1 ya wallafa: "Kaji tsoron Allah Bashir. Wannan hoton bai dace dakaiba."

@Kaneem7 ya wallafa: "Lokacin da Rahama Sadau ta wallafa hotonta, duk kuna ta yi mata ihu, amma yanzu babu wanda ke magana...koda yake Allah ya sanya al’khairi a auren.”

@Nrs_Idreeserh ya wallafa: “Hatta wadanda suka aibata Sadau da masu sa ido na nuna alamar san hoton da yi masu fatan alkhairi. Mu munafukai ne fa. Allah ya yafe mana kura-kuranmu.”

@GoalgetterJohn: “Abunda mutum zai fahimta shine cewa arewa ne munafirci sannan munafirci shine arewa. Lokacin da ake siyar da mai 100 duk sun yi zanga zanga a kan shugaba Goodluck Jonathan amma yanzu ba za su iya siyan famfon mai 170 sai dai ba za su taba fadin wani magana ta adawa da dayansu ba.”

A baya mun ji cewa Bashir El Rufai, daya daga cikin 'ya'yan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fitar da hotunan kafin aurensa inda ya nuna wa duniya matar da zai aura.

Bello El-Rufai ya wallafa hotunan kashi biyu a shafinsa na Twitter inda ya yi wa hotunan lakabi da 'My Nwakaego and I'.

Matar da zai aura, Halima Nwakaego Kazaure ita ma ta wallafa hotunansu tare da rubutu na shauki da bada takaitaccen tarihin haduwarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel