Zanga-zanga: Ya rage naku ku rungumi zaman lafiya, mu mun zo gangara - Buhari ga matasa

Zanga-zanga: Ya rage naku ku rungumi zaman lafiya, mu mun zo gangara - Buhari ga matasa

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed

- A yayin da ya ke yi wa tawagarta bayani a kan zanga-zangar ENDSARS, Buhari ya ce ruwan matasa ne su rungumi zaman lafiya

- Shugaba Buhari ya ce shi da sa'o'insa ta su ta zo karshe, sun kusa tafiya, a saboda haka zaman lafiya zi fi amfanar matasa

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da matasan da ke zanga-zangar ENDSARS a kan cewa ganin damarsu ce su rungumi zaman lafiya.

Buhari ya yi wa matasa tunin cewa rayuwarsa da ta sauran sa'o'insa ta zo gangara, a saboda haka, zaman lafiya matasa zai fi yi wa rana.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya (UN), Amina J. Mohammed, tsohuwar ministar muhalli a Najeriya.

DUBA WANNAN: NYSC: Buhari ya sake yi wa matasan da ke hidimtawa kasa goma ta arziki

"Mu tamu ta zo karshe, gangarawa muke, mun kusa tafiya," kamar yadda shugaba Buhari ya fada yayin martani a kan zanga-zangar ENDSARS.

Zanga-zanga: Ya rage naku ku rungumi zaman lafiya, mu mun zo gangara - Buhari ga matasa
Buhari
Asali: Facebook

A cewarsa; "alhakin matasa ne su rungumi zaman lafiya. Su na bukatar aiki da abubawan more rayuwa.

DUBA WANNAN: Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram

"Na aika shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Gambari, ya zagaya ko ina a kasar nan, ya tattauna da sarakunan gargajiya, wadanda su kuma zasu tattauna da matasa. Mun saurari bukatun matasa."

A nasa bangaren, Amina ta ce ta zo Najeriya ne tare da tawagarta domin domin nazarin wasu kalubale da UN ta damu da su, musamman annobar korona, sauyin yanayi, tsaro, da sauransu.

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) a kan ta tabbatar da shigar da matasan da ke hidimatawa kasa cikin tsarin cin moriyar inshorar lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel