Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram

Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram

- Wato kotun kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta zartar da hukunci a kan wasu 'yan Najeriya shidda

- Ana zargin mutanen da yin amfani da kudadensu wajen daukar nauyin ayyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram

- Biyu daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari, sauran hudun kuma daurin shekara goma

Wata kotun tarayya a Abu Dhabi Dubai, ta yankewa ƴan Najeriya shidda hukunci bisa zarginsu da ɗaukar nauyin Boko Haram, kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya gano kuma ya wallafa.

Biyu daga cikin waɗanda ake zargin, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf an yanke musu hukuncin zaman gidan yari iya tsawon rayuwarsu.

Su kuwa sauran mutane huɗun da suka haɗar da; Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf, da Muhammad Ibrahim Isa, dukkansu an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara goma.

KARANTA: A'a Farfesa: Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Waɗanda ake zargin,acewar tuhumar Kotun da jaridar Daily trust ta gano,ana tuhumar masu laifin tun shekarar 2019.

Sunayensu: An yankewa ƴan Najeriya 6 hukunci a UAE bisa ɗaukar nauyin Boko Haram
Tubabbun 'yan Boko Haram a Najeriya
Asali: Twitter

Kotun ta gano cewar daga shekarar 2015 zuwa 2016, waɗanda ake zargin sun tura zunzurutun kuɗaɗe har Dala $782,000 zuwa ƙungiyar Boko Haram, sai dai makusantan wadanda ake zargin sun ce an tura kuɗin ne a bisa halal ba don daukan nauyin ayyukan ta'addanci ba.

KARANTA: An ceto 'yammatan Katsina 26 daga hannun 'yan bindigar Zamfara

Sama da shekaru 11 da suka gabata, ana fama da ruɗani gami da sarƙaƙiya akan masu d'aukar nauyin k'ungiyar.

Wannan shine kusan karo na farko da aka gano masu aikata hakan a wajen Najeriya.

Wani babba daga jami'i a cikin gwamnatin Najeriya yace sun san da kwanan zancen.

Har yanzu gwamnatin tarayya ba ta sanar da sunaye balle ta zartar da hukunci a kan ma su daukar nauyin kungiyar Boko haram ba duk da rundunar soji ta sha ikirarin cewa sun san ma su yin hakan.

A makon da ya gabata ne Legit.ng ta wallafa cewa rundunar sojin saman Nigeria (NAF) ta ce zata tura da jiragen sama marasa matuki zuwa jihar Zamfara don bunkasa aikinta na yaki da 'yan bindiga a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel