NYSC: Buhari ya sake yi wa matasan da ke hidimtawa kasa goma ta arziki

NYSC: Buhari ya sake yi wa matasan da ke hidimtawa kasa goma ta arziki

- Shugaban hukumar NYSC, Janar Shuaibu Ibrahim, ya sanar da wani gata da shugaban kasa, Buhari, ya yiwa matasan da ke butar kasa

- A cewar Janar Ibrahim, shugaba Buhari ya bayar da umarnin a saka matasan da ke butar kasa a cikin tsarin inshorar lafiya ta kasa

- Kazalik, ya ce hukumar NYSC ta sake karfafa hadin gwuiwa da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro ga matasa 'yn bautar kasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) a kan ta tabbatar da shigar da matasan da ke hidimatawa kasa cikin tsarin cin moriyar inshorar lafiya.

Babban darektan hukumar kula da shirin bautar kasa (NYSC), Janar Shuaibu Ibrahim, ya sanar da hakan ranar Litinin.

Janar Ibrahim ya bayyana cewa NYSC ta kara karfafa alakarta da hukumomin tsaro domin tabbtar da tsaron lafiyar matasan da ke shirin NYSC a duk inda aka turasu.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003

Shugaban na NYSC ya bayyana hakan ne yayin wani taro manema labarai da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja.

NYSC: Buhari ya sake yi wa matasan da ke bautar kasa goma ta arziki
NYSC: Buhari ya sake yi wa matasan da ke bautar kasa goma ta arziki
Asali: Instagram

A cewarsa, hukumar NYSC ta na yaye matasa fiye da 300,000 a kowanne rukuni, wanda hakan ''ko shakka ya saka NYSC wani babban shiri na horon matasan Najerriya domin samun hadin kai da cigaba."

"Ina son yin amfani da wannan damar domin sake mika godiyarmu ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bamu.

DUBA WANNAN: A'a Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

"Bayan haka, NYSC ta kammala shiri da hukumar NHIS domin shigar da matasan da ke hidimar kasa cikin tsarin cin moriyar inshorr lafiya kamar yadda shugban kasa ya bayar da umarni," a cewar Janar Ibrahim.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Charles Agulanna, babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) bisa zarginsa da rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng