Sai inda karfinmu ya kare a kan makarantun Jami’a inji Shugaban ASUU

Sai inda karfinmu ya kare a kan makarantun Jami’a inji Shugaban ASUU

- Shugaban ASUU ya maidawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari martani

- Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce Kungiyar ASUU za ta tashi ta kare Jami’o’i

- Malaman jami’a sun ce ba a isa a hana su albashinsu a kan rajistar IPPIS ba

A ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce malamai sun shirya kare martabar jami’o’i.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa a shirye ASUU ta ke takawa gwamnatin tarayya burki na yunkurin murkushe jami’o’i da ta ke yawan yi.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, ya yi wannan jawabi ne a garin Ibadan, ya na mai maida martani ga jawabin da shugaban kasa ya yi a jiya.

KU KARANTA: Yajin - aiki : Babu maganar komawa makaranta - ASUU

Biodun Ogunyemi ya yi wa mai girma Muhammadu Buhari raddi na cewa ba za a biya duk wani malamin makarantar da bai yi rajista da IPPIS ba.

Farfesan ya tunawa shugaban kasar cewa ana bada wannan umarni ne ga sauran ma’aikatan gwamnati, domin malaman jami’a a sahu dabam su ke.

ASUU ta ce ta yi magana da shugaban kasa a Junairun 2020, inda su ka fahimci juna cewa za su kirkiri manhajar UTAS da za a rika biyansu albashi.

Ogunyemi ya ce babu dalilin da zai sa Muhammadu Buhari ya yi maganar da ya yi jiya, bayan ya amince su kirkiri manhajar da za ta yi aiki a kan malamai.

Sai inda karfinmu ya kare a kan makarantun Jami’a inji Shugaban ASUU
Shugabannin ASUU a taro Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

KUU KARANTA: Buhari ya biya malaman jami'a albashin watanni

A cewarsa sun gabatar da manhajar a ma’aikatar kudi, kuma su na jira su nunawa ma’aikatar tattalin arziki aikin da su ka yi bayan sun kashe miliyoyi.

A dalilin haka ne Farfesa Ogunyemi ya ce shugaban kasa bai isa ya ce ba zai biya malamai ba. Ya kuma shirin da aka kawo ya taba martabar jami’o’in kasar.

A jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa 'yan majalisa cewa ma'aikatan gwamnatin da ba su cikin manhajar IPPIS ba su da rabo a kasafin kudin kasa.

A gefe guda, ASUU ta ce ta samar da wata manhajar da ta fi dacewa da malaman jami'a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel