Da duminsa: An tashi baram baram a ganawar ASUU da FG kan janye yajin aiki
Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu a dai dai wannan lokaci na nuni da cewa an tashi baram baram a zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU.
Kungiyar malaman jami'o'i da gwamnatin tarayya sun shiga ganawa a ranar Alhamis, da zummar kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shiga.
Da farko, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayar da haske kan cewar a shirye malaman jami'o'in su ke su koma koyarwa.
KARANTA WANNAN: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19
Ya bayar da tabbacin ne biyo bayan alkawarin da ministan kwadago da daukar aiki, Dr. Chris Ngige ya bayar a wajen taron, na cewar gwamnati za ta cika burin kungiyar.
KARANTA WANNAN: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure
Sai dai, a daren ranar Alhamis, gidan talabijin na TVC News, ya ruwaito cewa, an tashi baram baram a karshen taron, ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
A wani labarin, A ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara shirin ruguza hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu da suka hada da EFCC da kuma ICPC.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisar, mai taken: "Dokar hukumar gurbattun kudade".
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng