Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

- Dattijo Amos Iyari Monye, tsohon soji mi mukmin kaftin, ya bayyana irin halin kunci da matsin rayuwa da ya ke ciki

- Tsohon sojan ya byar da tarihin yadda ya bautawa Najeriya a karkashin tsofin shugabannin kasa uku

- A cewar Monye, ya fi shakuwa da sabawa da shugankasa, Muhammadu Buhari, a cikin dukkan tsofin shugabannin kasa da ya yai aiki tare da su

Kaftin Amos Iyari Monye mai ritaya ya bayyana irin halin kunci da wahalar rayuwa da ya shiga duk da sallama rayuwarsa da ya yi domin kare Najeriya lokacin yakin basasa.

Kaftin Monye yace an harbe Shi lokacin da ake yakin inda da k'yar ya samu ya tsira da rayuwarsa.

''A ranar 27 ga watan Satumba shekarar 1963 na shiga aikin soja a jihar Oyo. An turani wurin horon aikin soja inda na shafe watanni shida ina kar'bar horo a aikin.

"Bayan kammala horonmu a watan Afirilu na shekarar 1964, an turani bataliya ta biyu da ke Jihar Abeokuta.

''Na shiga hadari mai yawa sakamakon aikina, bazan manta lokacin da akayi juyin mulki na biyu ba Wanda Janaral Murtala Muhammad ya jagoranta ba.

KARANTA: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi shagube a kan tsine mata a Masallatai

''Na wahala sosai saboda tunanin da Hausawan sojoji ke yi ni d'an k'abilar Igbo ne. Da k'yar na samu na ku'buta bayan sun tabbatar ni ba d'an yankin k'abilar Igbo bane.

''Na yi aiki da manyan sojoji Wanda daga baya duk sun shugabanci k'asar na.

''Na yi aiki da Janaral Yakubu Gowon, tsohon shugaban k'asa a mulkin soja, Janaral Olusegun Obasanjo tsohon shugaban k'asa wanda yayi mulkin soja da kuma farar hula, sai kuma Janaral Muhammad Buhari.

Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya
Kaftin Monye Mai ritaya @Punch
Asali: Twitter

''Amma kaf ba Wanda nafi kusanci da shi kamar Buhari. Ya san kusan komai, ko kuma na ce dukkan, wahalhalun da nasha," a cewarsa

Kaftin Monye ya ce an kore shi daga aikin soja a shekarar 1975 tare da wasu abokan aikinsa bisa zargin ha'inci da almundahana da kud'ad'e ba tare da wani bincike ba.

''Wannan shine rashin adalci mafi girma da aka tab'a yi min a rayuwata, k'asar da na sallama rayuwata akanta ta juya min baya.

''Duk wani yunkuri na ganin na wanke kaina daga zargin ya ci tura. Sun k'i sauraron mu. Ba mu da uban gidan da zai tsaya mana a maida mu aikin mu ko a biyamu hakkokinmu.

''Na sha matuk'ar wahala rayuwa, bani da ko gidan kaina, kuma ba zan iya kama gidan haya ba saboda halin babu da rashin kud'i.

KARANTA: Tamu ta samu: Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karrama wata 'yar sandan Nigeria

''Na zauna a gida mai daki d'aya na wani abokin aikina da muka yi zaman amana tare, ya bani aro.

''Babu ko gado a ciki, haka nake kwana a dindibiryar k'asa.

''Abincin da zan ci ma Saida ya gagareni, na zo ina rok'o a taimaka min.

''Ina roko ga mutane ukun nan da su taimaka min su ji k'aina.

''Yanzu haka inada ƴaƴa guda biyu kuma duk sun kammala karatunsa amma babu aikin yi haka muke fama tare da su. Muna ta shan wahalar gwagwarmayar rayuwa," a cewar Kaftin Monye.

Su kuwa Dakarun rundunar sojin kasar Amurka sanarwa suka fitar cewa sun kubutar da wani Ba-Amurke da 'yan bindiga suka boye a arewacin Najeriya bayan an yi garkuwa da shi a makon jiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel