Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020

Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020

- Hukumar WAEC ta sanar da sakin sakamakon jarabawar daliban da suka zauna a wannan shekarar

- Kamar yadda shugaban hukumar na Najeriya ya sanar, kashi 65.24 sun samu nasara har a darussan Lissafi da Turanci

- Ya kara da cewa, kashi 13.98 wanda yayi daidai da dalibai 215,149 ne aka rike wa sakamakonsu

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantar sakandire ta kasashen Afrika na yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarrabawar shaidar kammala sakandire (SSCE) na shekarar 2020.

Tun ranar Lahadi WAEC ta yi alkawarin cewa za ta saki sakamakon jarrabawar ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba.

Matakan duba sakamakon jarrabawar basu da wahalar fahimta ga duk dalibin da zai duba sakamakonsa.

Dalibi yana bukatar katin shaidar rubuta jarrabawa mai dauke da wasu muhimman lambobi, ana bukatar wadannan lambobi domin duba sakamakon jarrabawar WAEC.

Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020
Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC ta 2020 @legit.ng
Asali: Twitter

Ga jerin matakai 7 da mutum zai bi kamar haka;

1. Ziyarci adireshin yanar gizo na shafin WAEC da ake duba sakamakon jarrabawa https://www.waecdirect.org.

2. A rubuta lambar WAEC a gurbin da aka samar a shafin

3. Sai a zabi shekarar da aka rubuta jarrabawa

4. A cike sunan irin sakamakon da ake son dubawa, wato ''school candidate result''

5. Sai a shigar da lambar katin jarrabawa

6. A shigar da muhimman lambobin katin jarrabawa (PIN)

7. Sai mutum ya latsa makulin 'aike' (Submit) domin ganin sakamakon jarrabawarsa na WAEC din 2020

KARANTA: kuɗin ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i

A baya Legit.ng Hausa ta wallafa cewa hukumar WAEC ta saki sakamakon jarabawar daliban da suka kammala babbar makarantar sakandare a wannan shekarar.

Shugaban hukumar reshen Najeriya, Patrick Areeghan ya sanar da hakan a ranar Litinin a garin Legas, Premium Times ta wallafa.

Kamar yadda yace, dalibai 1,003,668 da ke wakiltar kashi 65.24 na dukkan daliban da suka rubuta jarabawar sun samu sakamako mai kyau a darussa biyar da suka hada da darasin Turanci da Lissafi.

Ya ce dalibai 1,338,348 da suka rubuta jarabawar wanda suke wakiltar kashi 86.99 na jimillar daliban sun samu nasara a a kalla darussa biyar.

KARANTA: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

Patrick Areghan ya sanar da cewa, hukumar ta rike sakamako 215,149 na daliban da suka rubuta jarabawar a wannan shekarar.

Kamar yadda yace, sakamakon da aka rike na wakilatar kashi 13.98 na jimillar wadanda aka saki. Ammaa halin yanzu ana binciken sakamakon wadanda ake zargi da satar jarabawa.

Ya ce dalibai 1,549,740 ne suka yi rijistar jarabawar a wannan shekarar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel