kuɗaɗen ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i

kuɗaɗen ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i

- Tun a cikin watan Satumba gwamnatin tarayya ta bude shafin yanar gizo domin jama'a su nemi tallafi daga kudaden ceto, N75bn, da aka ware

- Sai dai, al'amura sun ki tafiya yadda ya kamata tun bayan bude shafin tare da sanar da jama'a adireshinsa domin su nemi tallafin

- Gwamnatin tarayya ta ce ta sauya adireshin shafin kuma zai koma kan sabon turken yanar gizo daga ranar 1 ga watan Nuwamba

Gwamnatin tarayya tace za ta sauya adireshin yanar gizo na shafin neman tallafin Ƙanana da matsakaitan sana'o'i (SMEs survival fund) da kuma tsarin Guaranteed off-take Stimulus Scheme daga 1 ga watan Nuwamba.

A cewar gwamnati, ta yi hakan ne sakamakon ƙalubalen gudarnarwa da suke fuskanta a kan adireshin farko da aka turke shafin a kansa a yanar gizo.

Ambasada Maryam Katagum, Ministar Kasuwanci da massna'antu kuma shugabar kwamitin tsarin tallafin ceton ƙanana da matsakaitan sana'o'i (MSME survival fund) da kuma Guaranteed off-take Stimulus Scheme, ita ce ta bayyana hakan ranar Asabar a garin Abuja.

KARANTA: Sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan bindigar arewacin Najeriya a kan Ba-Amurke guda daya

Acewar ministar, adireshin yanar gizon na neman tallafin zai sauya matsuguni zuwa www.survivalfund.gov.ng daga ranar 1 ga watan Nuwamba.

kuɗaɗen ceto: Gwamnatin ta sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin ƙanana da matsakaitan sana'o'i
Ambasada Maryam Katagum @Thenationnews
Asali: Twitter

"Ina mai sanar da kafatanin al-umma, sakamakon matsalar gudanarwa, kwamitinmu zai sauya adireshin yanar gizo na neman tallafin kanana da matsaikaitan sana'o'i daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa www.survivalfund.gov.ng.

"Ana gargaɗin jama'a cewa kada su bawa kowa kudinsu da sunan zai taimaka musu don cin moriyar tallafin," a cewar ministar yayin da take tabbatarwa da jama'a cewa komai kyauta ne.

KARANTA: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa survival fund tallafi ne don ceton wanda annobar Korona ta shafa a kanana da matsaikaitan sana'o'in su, don farfaɗo da sana'o'i da da ceto ayyuka da rage radaɗin karyewar tattalin arziƙin kasuwan da 'yan kasuwa.

A yayin ranar 27 ga watan Oktoba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki ta hanyar fara bayar da tallafin N30,000 ga mutum 300,000 a jihohi 10.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel