Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya bukaci hadin-kai bayan ya hau gadon sarauta

Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya bukaci hadin-kai bayan ya hau gadon sarauta

- Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi jawabi bayan zamansa Sarkin Zazzau

- Sabon Sarki ya ce ya na da kyakkyawar dangantaka da Katsinawa da Bareberi

- Mai martaba ya yi kira a fawwala lamari ga Ubangiji mai karfin bada mulki

Sabon sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya yi kiran hadin-kai a lokacin da ya yi jawabi, jim kadan da nada shi magajin Shehu Idris.

A wani gajeren bidiyo da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, an ji Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya na alkawarin cewa zai tafi da kowa a mulkinsa.

Ahmed Nuhu Bamalli ya yi jawabi ne a fadarsa bayan an sanar da nadin shi a matsayin Sarki na 19 a masarautar Zazzau a ranar Laraba, 7 ga Oktoba.

Mai martaba ya bayyana cewa ya na da alaka ta kusa da sauran gidajen Katsinawa da Beriberi.

KU KARANTA: Magajin Garin Zazzau ya tsallake siradin mulki, ya zama Sarki

“Ina da alaka mai kyau da duka gidajen Zazzau.” Mai martaba ya ce bayan haka, akwai mutuncin juna da ake gani tsakanin gidajen da ke sarauta a kasar.

“Mai daki na ta fito ne daga gidan Katsinawa domin ‘diyar Marigayi Sarkin Zazzau, Shehu Idris. Kakannina daga bangaren uwa, jinin Bareberi ne.”

“Don haka ban ga abin da zai sa in samu sabani da wadannan gidaje ba.” Inji Sarki Bamalli.

“Ubangiji ne ya ke bada Sarki, ba kudin mutum ba ne, ko dukiyarsa, ko karfin mulki.” Sarkin ya ke fada a wannan gajeren jawabi da ya yi ba da dadewa ba.

Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya bukaci hadin-kai bayan ya hau gadon sarauta
HRH Ahmed Bamalli Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: An samu wanda ya ajiye rawaninsa a masarautar Zazzau

Sabon Sarkin ya cigaba da cewa: “Idan da wadannan ne su ke bada mulki, da watakila ba mu zo inda mu ke yau ba." Ya ce Allah ne ya ke bada mulki.

Sarkin ya ce ya ji dadi da ya ga gidajen Katsinawa da Barebari sun yi mubaya’a. Ya ce zai yi kokarin hada-kan mutanen Zazzau a kankanin lokaci.

Tun a jiya kuma mu ka ji cewa Yariman Zazzau, Muhammadu Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Nuhu Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau.

Yariman Zazzau wanda ya na cikin masu neman sarautar Zazzau ya amince da naɗin Bamalli.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel