Sanusi: Ko da babu dadi, an yi daidai da aka yi watsi da biyan tallafin man fetur

Sanusi: Ko da babu dadi, an yi daidai da aka yi watsi da biyan tallafin man fetur

Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce abin da gwamnatin tarayya ta yi wajen farfado da tattalin arzikin kasa ya yi daidai.

A karshen makon nan ne aka rahoto tsohon sarkin ya na cewa tun kafin a gamu da annobar COVID-19, ya kamata gwamnati ta dauki wadannan matakai.

Da ya ke magana a gidan talabijin Arise TV a ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, Sanusi II ya ce cire tallafin man fetur da aka yi, shi ne abin da ya dace.

“Wadansu matakai da ake dauka kwanan nan, wadanda aka aro daga IMF na cire tallafin man fetur, duk da zafin yin hakan, su ne abubuwan da su ka dace ayi idan ana so kudin asusun gwamnati su karu.”

Sanusi II ya kara da cewa: “Yanzu an samu karuwar gaskiya a hukumar NNPC.”

“Na ji cewa NNPC ta zuba kusan Naira tiriliyan biyu a asusun FAAC, wanda wannan ya fi abin da aka tara a tsawon shekaru.”

KU KARANTA: Gwamnan Ogun ya yi magana kan karin kudin man fetur

Sanusi: Ko da babu dadi, an yi daidai da aka yi watsi da tallafin man fetur
Sanusi ya yabi janye tallafin man fetur
Asali: Facebook

Mai martaba ya ke cewa idan aka samu gaskiya wajen sha’anin mai, za a ga canji a sauran bangarorin gwamnati.

Sai dai duk da nuna goyon baya da tsohon gwamnan na CBN ya bada na zare tallafin mai, ya ce akwai gyara a lamarin yadda kasar ta ke kashe kudi.

“Gwamnati ta duba yadda ta ke batar da kudi, ta tabbatar cewa ya na kai wa ga talakawan kasa.”

A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta rika kashe kudi ne a harkar ilmi, ruwan sha, cigaban karkara, ya ce wannan ya fi muhimmanci a kan gina gidaje da gada.

Kafin annobar COVID-19, Sanusi II ya ce tattalin arzikin kasar ba ya motsawa sosai saboda biyan bashi da makudan kudin tallafin mai da Najeriya ta ke yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel