Sojoji su na so su yi mulkin rikon kwarya na tsawon shekaru 3 a kasar Mali - Majiya

Sojoji su na so su yi mulkin rikon kwarya na tsawon shekaru 3 a kasar Mali - Majiya

- Sojojin Tawaye sun amince su saki shugabannin kasar Mali da su ke tsare

- ECOWAS ta na so a maida Shugaba Ibrahim Keita ya koma kan karagar mulki

- Sojojin da su ka yi juyin mulki su na so su jagoranci gwamnatin rikon kwarya

Sojojin da su ka kifar da gwamnatin kasar Mali su na so su yi mulkin rikon kwarya na shekaru uku kafin shugabanci ya koma hannun farar hula a kasar.

Wata majiya daga tawagar shugabannin kasashen yammacin Afrika da ta gana da sojojin tawaye na kasar Mali ta bayyana wannan a ranar Lahadin da ta gabata.

A makon da ya wuce ne aka yi juyin mulki a kasar Mali, wannan shi ne karo na biyu da aka yi yunkurin hambarar da gwamnati a kasar Afrikan a cikin shekaru takwas.

“Sojojin tawaye sun tabbatar da cewa su na son su rike gwamnati na shekaru uku. Sojoji za su shugabanci wannan gwamnatin rikon kwarya da za a kafa.”

Wani cikin 'yan tawagar Goodluck Jonathan da ta gana da ‘yan tawayen ya bayyanawa AFP haka. Majiyar ta ce za a samu shugaban soji da zai rike gwamnati.

KU KARANTA: Juyin-mulki: ECOWAS ta hana kasashe duk wata alaka da Mali

Sojoji su na so su yi mulkin rikon kwarya na tsawon shekaru 3 a kasar Mali - Majiya
Sojojin Tawayen kasar Mali
Asali: UGC

“Sojoji ne kuma za su cika gwamnatin (rikon-kwaryar).” Wanda ya bayyanawa ‘yan jarida wannan shiri da ‘yan tawayen su ke yi, ya bukaci a sakaya sunansa.

Haka zalika sojojin sun amince su fito da tsohon shugaba Ibrahim Keita, wanda aka tursasa ya yi murabus, tare da duk sauran shugabannin farar hula da ke tsare a Bamako.

“Kuma idan ya na so ya tafi kasar waje neman magani, wannan ba matsala ba ce.”

Yayin da tawagar Jonathan ke kokarin shawo kan rikicin siyasar Mali, sojojin da su ka hambarar da gwamnati sun ce za su gudanar da zabe a kasar nan da wani lokaci.

A daidai wannan lokaci shugabannin Afrika na kungiyar ECOWAS su na kiran a maida Ibrahim Keita kan mulki, ya karasa wa’adinsa na shugaban kasa da ya fara a 2018.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel