‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa 3 da wasu mutum biyu a Taraba

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa 3 da wasu mutum biyu a Taraba

'Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace 'yan kasuwa uku da masu achaba biyu a sa'o'in farko na ranar Litinin.

Sun yi garkuwa da mutanen ne a hanyar babban titin Dananacha-Borno-Kurukuru a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan kasuwar na kan baburan haya ne a hanyarsu ta zuwa kasuwar sati ta Borno Kurukuru.

An gano cewa 'yan kasuwar na dauke da makuden kudade yayin da suka ci karo da 'yan bindigar da suka tsare titin.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa 3 da wasu mutum biyu a Taraba
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa 3 da wasu mutum biyu a Taraba Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Titin mara kwalta ya shiga har cikin dajin da zai sada jama'a da kasuwar satin.

Ya kasance tashin hankalin matafiya saboda 'yan bindiga sun mayar da shi wurin zama da garkuwa da mutane.

A lokacin rubuta wannan rahoton, ba a ga ko kurar wadanda aka sace ba.

Bayan tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce har yanzu bai samu rahoton aukuwar lamarin ba.

KU KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun damke dattijo mai shekaru 48 da ya yi wa yarinya fyade

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu.

An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, jaridar Daily trust ta ruwaito.

'Yan bindigar da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi.

Malamin kuma babban dan sandan, na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba.

An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar ranar Juma'a.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin nan.

An gano cewa, wuraren da abun ya shafa sun hada da kusa da gadar Donga, Baba Yau, Mile 6, Kona, Wuro Sambe, Sabongari da yankin firamare.

An gano cewa mazaunan yankin ne cike da tsoro tare da fargabar masu garkuwa da mutanen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel