Taraba: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda

Taraba: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda

- ‘Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu

- Maharan da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar daren Lahadi tare da sace shi

- A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba

'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu.

An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, jaridar Daily trust ta ruwaito.

'Yan bindigar da za su kai 10 sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi.

Malamin kuma babban dan sandan, na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba.

An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar ranar Juma'a.

A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin nan.

An gano cewa, wuraren da abun ya shafa sun hada da kusa da gadar Donga, Baba Yau, Mile 6, Kona, Wuro Sambe, Sabongari da yankin firamare.

An gano cewa mazaunan yankin ne cike da tsoro tare da fargabar masu garkuwa da mutanen.

Taraba: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda
Taraba: 'Yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sanda Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wani mazaunin kusa da fadar Donga mai suna Mathew Bulus, ya ce a yan kwanakin da suka gabata, wani ma'aikacin PHCN, Joseph Zaphania ya shiga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ya kara da cewar mutumin ya kuma mutu kwanaki kadan bayan da suka sako shi.

Ya ce 'yan bindigar sun kutsa yankin har sau uku a makon da ya gabaga amma sun yi yunkurin sace wani mai kudi,wanda hakan bai yuwu ba.

An gano cewa, mutane da yawa a yankin sun shiga hannun 'yan bindigar amma an sako su bayan biyan kudin fansa.

KU KARANTA KUMA: Magu: Yadda ake kwashe 'ruwan' N550bn da EFCC ta kwato

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce bashi da bayanin aukuwar lamarin.

"Bani da bayanin nan a halin yanzu. Ku bani lokaci," DSP Misal yace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng