Mele Kyari zai kawo gyaran da Najeriya ta ke bukata a NNPC - Gwamna El-Rufai

Mele Kyari zai kawo gyaran da Najeriya ta ke bukata a NNPC - Gwamna El-Rufai

A ranar Juma’a ne kamfanin man Najeriya na NNPC ya fitar da rahoton diddikin kudin da aka kashe.

Wannan ne karon farko da aka yi wannan a cikin shekaru 43 da kafuwar kamfanin.

Rahoton da aka fitar ya tike ne da karshen Dismaban 2018, inda ya nuna yadda sauran kamfanoni 20 da ke karkashin NNPC su ke gudanar da aikace-aikacensu a cikin gida da wajen Najeriya.

Kamfanonin da aka bayyana abin da su ke samu da abin da su ka kashe sun hada da kamfanonin tatar mai na NPDC, WRPC, PHRC, KRPC da ke garuruwan Fatakwal, Warri, da kuma Kaduna.

Sauran kamfanonin sun hada da IDSL, NPMC da NPSC masu saida kayan mai da kuma adana mai a bututun kasa. Har ila yau akwai kamfanoni irinsu NETCO, NGMC, UK, NAPIMS, da NIDAS.

Wannan aiki da NNPC ya yi a karkashin Malam Mele Kolo Kyari ya jawowa kamfanin yabo daga wurare da-dama a kasar. Tun asali wannan ya na cikin alkawarin da Mele Kyari ya dauka.

KU KARANTA: Abin da ya sa za mu kara kudin wutar lantarki - Ministan wuta

Mele Kyari zai kawo gyaran da Najeriya ta ke bukata a NNPC - Gwamna El-Rufai
Shugaban NNPC na kasa, Mele Kolo Kyari Hoto: Headtopics
Asali: UGC

Haka zalika shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari a 2014 cewa idan ya hau kan mulki, za a fadawa Duniya hakikanin gaskiyar abin da NNPC ta ke samu, da abin da ta ke batarwa.

Shugaban kamfanin da ke binciken arzikin man fetur a kasa watau NEITI, Waziri Adio, ya taya Mele Kyari murnar alkawarin da ya cika, ya yi kira da a cigaba da yin wannan ke-ke-da-ke-ke.

Shi kuwa Nasir El-Rufai cewa ya yi: "Zuciyar Mele Kyari ta na inda ta dace! Wa’adinsa a ofis zai canza salon yadda abubuwa su ke tafiya a kamfanin NNPC da abin da Najeriya ta ke bukata."

Gwamna Nasir El-Rufai ya kara da cewa: “Ya kware a aiki, ya san abin da ya ke yi, kuma ya na toshe kafar sata, tare da kafa kamfanin a kan hanyar gaskiya da kuma yin ke-ke-da-ke-ke.”

Mai girma gwamnan ya bayyana cewa miyagun da su ke cin karensu babu babbaka a harkar mai ba za su kyale shugaban na NNPC ba. Ya ce: “Dole miyagun gidan mai za su kai masa hari.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel