Ahmad Lawan: Abin da ya sa Najeriya ta gaza cin yaki da ‘yan ta’adda

Ahmad Lawan: Abin da ya sa Najeriya ta gaza cin yaki da ‘yan ta’adda

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya alakanta gazawar sojojin Najeriya da jami’an tsaro wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da harkar siyasar kasashen Duniya.

Ahmad Lawan ya yi magana ne da ‘yan jarida a karshen makon da ya gabata, inda ya zargi siyasar kasashen Duniya da hannu wajen kin bari a saidawa jami’an tsaro kayan yaki.

Lawan ya ke cewa rashin samun manyan makaman da ake bukata ya kawowa jami’an tsaro cikas.

Da ya ke yi wa manema labarai bayani, sanata Dr. Ahmad Lawan ya ce ana batawa dakarun sojojin Najeriya lokaci fiye da yadda ya kamata kafin su iya fansar makaman yaki.

Shugaban majalisar ya ke cewa aiki ya yi sojojin Najeriya yawa, sannan kuma akwai bukatar a tanadi kayan yaki kafin a iya shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da shi.

“Kusan ka iya cewa mu na fama da matsalar siyasar Duniya. Na san cewa wajen kokarin sayen kayan jiragen yaki, ya kan dauke mu tsawon lokacin watanni shida ko ma tara.”

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kona gidaje bayan kashe mutane 60 a Borno

Sanatan ya ce akwai rashin adalaci harkar ta ke tafiya: “Idan wata kasar ta rubutawa gwamnati takarda cewa ta na son makamai, sai a saida mata a cikin wata guda ko kuma biyu.”

“Saboda haka abubuwa ba su tafiya daidai, wannan ya na cikin kalubalen mu. Za mu cigaba da kokarin tattaunawa da wadannan kasashe da ba su gane inda mu ka dosa ba.”

“Jami’an tsaronmu kuma su na bukatar karin dakaru da kudi.”

“Mu na bukatar karin jami’an ‘yan sanda, masu kula da shige da fice da kusan duk wasu bangarorin tsaro.”

Dr. Lawan ya ke cewa Najeriya ta na kuma da bukatar ma’aikata. “Gwamnati ta na bakin kokari wajen samun kayan aiki da makamai.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel