A karkashin Jam’iyyar APC zan sake tsayawa takarar Gwamna – Godwin Obaseki

A karkashin Jam’iyyar APC zan sake tsayawa takarar Gwamna – Godwin Obaseki

- Godwin Obaseki ya tabbatar da cewa a APC zai nemi takarar a zaben bana

- Gwamnan Jihar Edo ya samu sabani da Shugaban APC, Adams Oshiomhole

Mai girma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya hakikance a kan sake neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a zaben da a za ayi nan da watanni hudu.

A jiya Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, Godwin Obaseki ya shaida cewa zai jarraba sa’arsa ne a zabe mai zuwa a jam'iyyar APC. Gwamnan ya yi wannan bayani ne a birnin tarayya Abuja.

Yayin da wata kungiya ta Magoya baya wanda ake kira Obaseki Mandate Group ta kai wa gwamnan ziyara, ya shaidawa masoyan na sa cewa zai tsaya a cikin jam’iyyar APC.

Idan ba ku manta ba a makon jiya ne wani jigo na PDP mai adawa a yankin kudancin Najeriya ya bayyana cewa kofa a bude ta ke ga gwamna Godwin Obaseki idan ya sauya-sheka.

KU KARANTA: Yadda mu ka yi da Shugaba Buhari da mu ka sa labule - Obaseki

A karkashin Jam’iyyar APC zan sake tsayawa takarar Gwamna – Godwin Obaseki
Shugaba Buhari da Godwin Obaseki Hoto: NgrPresidency
Asali: Facebook

Emmanuel Ogidi ya yi wa Godwin Obaseki tayi ganin yadda ya ke fama da rikicin cikin gida. A karshe gwamnan ya yi fatali da wannan zawarci, ya ce a APC za a gwabza da shi.

Obaseki ya bayyanawa ‘yan Obaseki Mandate Group a jiya cewa masoyansa a shirye su ke su da su saya masa fam din takara a kowace jam’iyyar siyasa ya bukaci ya nemi tsayawa.

Sai dai duk da wannan goyon baya da gwamnan mai-ci ya ke samu daga masoyansa, ya ce ya natsu da ya sake neman tikitin takara karkashin jam’iyyar da ta kawo shi kan mulki.

Rahotannin da mu ka samu daga jaridar Punch sun bayyana cewa gwamnan ya ji dadin yadda mutane su ka hada kudi, su ka saya masa fam din APC saboda ya cigaba da rike jihar.

A cewarsa ya shiga siyasa ne domin ya canzawa mutane ra’ayi na ganin cewa ‘yan siyasa mutane ne da ke neman mulki ta hanyar a mutu ko ayi rai, ya yi kira ga mutane su zabi na kwarai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel