Yanzu-yanzu: Obaseki ya je ganin Buhari yayinda Gwamnonin APC suka shiga taro mai matukar amfani

Yanzu-yanzu: Obaseki ya je ganin Buhari yayinda Gwamnonin APC suka shiga taro mai matukar amfani

A kokarin ceto Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, wasu gwamnonin jam'iyyar APC sun tsinkayi ofishin jam'iyyar a ranar Litinin don yin taron toshe baraka da Kwamared Adams Oshiomhole, jaridar The Nation ta ruwaito.

An sake shiga wani taron makamancin hakan da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu a garin Legas.

A halin yanzu ana ci gaba da taron a dakin taro da ke ofishin jam'iyyar da ke Abuja tare da shugaban jam'iyyar na kasa wanda ke jagoranci.

Gwamnonin da suka samu halartar taron sun hada da Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredoku, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa.

Sauran sune, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaki.

Har ila yau, Gwamna Godwin Obaseki ya gaggauta kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari fadarsa da ke Aso Villa a Abuja.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya kai ziyarar ne sakamakon zaben fidda gwani da ke tunkaro jiharsa da kuma rikicin da ke tsakaninsa da Kwamared Adams Oshiomhole a jihar Edo.

Ga bidiyon ziyarar da Obaseki ya kai ofishin Buhari:

KU KARANTA KUMA: Sokoto: FG ta yi kira ga cibiyoyi da su mika tallafi ga wadanda harin 'yan bindiga ya shafa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tun ganawar sirri tsakanin jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da gwamnonin jam'iyyar APC ya haifar da cacar baki mai zafi a dandalin sada zumunta.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya kira taron ne domin sulhunta rigingimun cikin jam'iyyar APC da ke kara zurfi, musamman a jihar Edo.

An dade ana nuna yatsa tare da musayar maganganu marasa dadi a tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Taron na sirri, wanda aka yi ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, ya samu halartar shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, gwaman jihar Ondo; Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Legas; Babajide Sanwo-Olu.

Ragowar sun hada da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar GAnduje, Godwin Obaseki na jihar Edo, Simon Lalong na jihar Filato, Mai Mala Buni na jihar Yobe, Adeboyega Oyetola na jihar Osun, Badaru Abubakar na jihar Jigawa, da Abubakar Bello na jihar Neja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel