Jihohi 25 a Najeriya wanda coronavirus ta bulla - NCDC

Jihohi 25 a Najeriya wanda coronavirus ta bulla - NCDC

Duk da irin kai ruwa rana da hukumomin lafiya ke yi domin hana yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, cutar tamkar wutar daji na ci gaba da bazuwa a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 25 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Talata 21 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 665 yayin da tuni mutane 188 suka samu waraka.

Ya zuwa yanzu dai mutane 22 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-376; Abuja-89; Kano-59; Osun-20; Oyo-16; Edo-15; Ogun-12; Kwara-9; Katsina-12; Bauchi-7; Kaduna-9; Akwa Ibom-9; Delta-4; Ekiti-4; Ondo-3; Enugu-2; Rivers-2; Niger-2; Benue-1; Anambra-1; Borno-3; Jigawa-2' Abia-2; Gombe-5; Sokoto-1.

Da misalin karfe 11.10 na daren ranar Litinin, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 38 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Hanyoyin kaucewa rushewar Najeriya da dokar hana fita za ta haifar

Jihohin da cutar ta bulla karo na farko a baya-bayan nan sun kasance Borno da Gombe a yankin Arewa maso Gabas, jihar Sakkwato a Arewa maso Yamma da Abia a yankin Kudu maso Gabas.

Sai dai kuma wani abu mai ban mamaki cikin alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Litinin shi ne, yadda ba samu karin wadanda cutar ta harba ba ko guda daya a jihar Legas.

Babu shakka annobar covid-19 ta fi kamari a jihar Legas, da kuma birnin Abuja a mataki na biyu sai kuma jihar Kano da ta biyo bayansu.

Mun ji cewa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya da ta kawo masa dauki na tallafin kudi domin saukaka radadin yakar wannan annoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel