Ka da a kawo siyasa a lamarin tsohon Sarki Sanusi Legas - Afenifere, YCE, YUF

Ka da a kawo siyasa a lamarin tsohon Sarki Sanusi Legas - Afenifere, YCE, YUF

Kungiyoyin Yarbawa irinsu Afenifere, Yoruba Council of Elders watau YCE da kuma Yoruba United Front sun yi magana game da hijirar da Muhammadu Sanusi II ya yi zuwa Legas.

Jaridat The Guardian ta bayyana cewa wadannan kungiyoyi na kabilar Yarbawa sun koka da siyasar da su ka ga wasu su na yi ta hanyar yi wa tsohon Sarkin na Kano fadanci a gidansa.

Manyan kungiyoyin Afenifere da YCE Yinka Odumakin da Dr. Kunle Olajide sun gargadi wadanda su ka maida gidan Muhammadu Sanusi wata Makkar Najeriya da su bi sannu a hankali.

Shi ma shugaban kungiyar YUF da Sakatarensa Alhaji Raimi Ali da Deacon Samuel Aderanti sun yi irin wannan gargadi da masu neman cusa siyasa a lamarin tsohon Sarkin da aka tsige.

Kungiyoyin sun yabawa kalaman da Muhammadu Sanusi II ya rika yi a ‘yan kwanakin nan, inda ya rika sukar shugabannin Arewa, amma duk da haka sun ce ba su manta wanene shi ba.

KU KARANTA: Sanusi II ya yi magana daga Legas, ya nemi ayi ta-ka-tsan-tsan da Coronavirus

Ka da a kawo siyasa a lamarin tsohon Sarki Sanusi Legas - Afenifere, YCE, YUF
Kungiyoyi sun ce ana maida gidan Sanusi II fadar siyasar 2023
Asali: Twitter

A cewar Afenifere da YCE, sun san tarihin tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya. Kungiyoyin sun ce wasu sun fara buga gangar siyasar 2023 a sabon gidan tsohon Sarkin.

Kungiyar Afenifere ta ce ko da Sanusi II ya yi gaskiya a wasu maganganu da ya yi tayi, sai dai a na ta ra’ayin, tsohon Sarkin na Kano mutum ne mai tsaurin ra’ayin kabilanci a Najeriya.

Ita ma kungiyar YCE ta ce babu wani abin nunawa game da halin Sanusi II na kishin kabilarsa. A na ta bangaren, YUF ta tunawa Duniya lokacin da Sanusi ya soki Yarbawan kasar nan.

A baya tsohon Mai martaban ya taba yin wani rubutu inda ya nuna Yarbawa ne matsalar Najeriya. Wannan ya sa kungiyar YUF ta ce ta yi mamakin ganin Sanusi II ya tare a Legas.

Haka zalika kungiyar ta ja ka kunnen shugabannin Yarbawa da su guji kyale Muhammadu Sanusi II ya kafa wata daular Fulani a Leas domin mutum ne mai tsananin kishin addini.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel