Dalilin da ya sa manyan APC su ka daga taron NEC da aka shirya yau

Dalilin da ya sa manyan APC su ka daga taron NEC da aka shirya yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwmanonin Jihohin APC sun zabi su dakatar da taron NEC da a baya aka shirya cewa za ayi a Ranar Talata, 17 ga Watan Maris.

Shugabannin APC sun dakatar da wannan taro na majalisar zartarwa zuwa wani lokaci. Shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu ya bayyana wannan Ranar Litinin.

Daily Trust ta ce Gwamnan jihar Kebbin ya dakatar da wannan zama na NEC ne domin hana jam’iyyar wargajewa a sakamakon rikicin gidan da ake fama da shi a yanzu.

Wata majiya daban ta bayyana cewa har yanzu wadanda ba su tare da Adams Oshiomhole sun koma gefe guda su na tsara yadda za a tsige shugaban jam’iyyar a wannan zama.

Kafin sa bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari a farkon makon nan, Jaridar ta bayyana cewa ana ganin za a yi amfani da majalisar NEC wajen tunbuke Adams Oshiomhole.

KU KARANTA: NWC: Majalisar Oshiomhole za ta yi zama a Ranar Talata a Sakariyar APC

Dalilin da ya sa manyan APC su ka daga taron NEC da aka shirya yau
Gwamnan APC ya ce an dakatar da taron NEC sai wani lokaci
Asali: Facebook

Gwamnan jihar Edo watau Godwin Obaseki da wasu gwamnonin APC wanda ba su da rinjaye ne su ke kutun-kutun na ganin an yi waje da Oshiomhole daga kujerarsa.

Babban Jigon APC a Kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, da Magoya bayansa su na cikin wadanda ke marawa shugaban jam’iyyar ta APC na kasa baya a yanzu.

Yanzu dai ana shirya lokacin da majalisar ta NEC za ta zauna inda za a gayyaci kwamitin Bisi Akande ya yi bayani game da harnyar da za a dinke barakar Jam’iyyar.

A cewar Gwamna Atiku Bagudu, shugaban kasa Buhari ya goyi bayan a dakatar da wannan zama har sai zuwa lokacin da gwamnonin APC su ka zauna su ka fitar da matsaya.

A daidai jiyan ne kuma kotun daukaka kara ta ba Adams Oshiomhole nasara bayan a baya an dakatar da shi daga kujerarsa. Wannan ya sa Majalisar NWC za ta zauna yau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel