Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a (Hotuna)

Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a (Hotuna)

- Korarren sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya samu yanci inda zai garzaya jahar Lagas

- A yanzu haka tsohon sarkin zai gabatar da sallar Juma’a a garin Awe da ke jahar Nasarawa, kamar yadda mutanen yankin suka bukata

- Bayan sallar Juma'a ne tsohon sarkin da Gwamnan jahar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai Za su tafi Abuja, inda daga nan zai kama hanyar zuwa jahar Lagas

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa korarren sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya samu yanci inda zai garzaya jahar Lagas.

An tattaro daga Wata majiya mai karfi cewa a yanzu haka tsohon sarkin zai gabatar da sallar Juma’a a garin Awe da ke jahar Nasarawa, kamar yadda mutanen yankin suka bukata.

Daga nan ne kuma tsohon sarkin da Gwamnan jahar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai Za su tafi Abuja, inda daga nan zai kama hanyar zuwa jahar Lagas.

Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a
Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan umurnin da Wata babbar kotu a Abuja ta bayar na cewa a bari Sanusi ya shiga duk inda yake so a Najeriya amma ban da jahar Kano.

Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a
Yanzu Yanzu: Tsohon sarkin Kano Sanusi II ya samu yanci zai tafi lagas bayan sallar Juma’a
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Sanusi: Yan sanda sun kama sojan bogi a Awe

A baya mun ji cewa an fara shirye-shirye domin tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi limancin sallar Juma'a a garin Awe.

Wata majiya kwaƙwara ta shaidawa Daily Trust cewa an shirye-shirye domin bawa Sanusi limancin sallar Juma'a duk sati a garin. Masallacin Juma'ar tana hade ne da fadar Sarkin Awe, Alhaji Isa Abubakar Umar.

An kuma bayyana cewa an tsaurara matakan tsaro a yankin na Awe sakamakon shiga jama'ar da tsohon sark zai yi za lokacin sallar Juma'an.

Matasa sun fara tururuwa zuwa masallacin dauke da taburma da dadduma domin hallartar sallar ta Juma'a.

Idan ba manta ba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II shine ya ke limancin sallar Juma'a a Kano kafin a lokacin da ya ke sarauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel