Tsige Sanusi II: Farfesa Auwal Yadudu da Sanata Shehu Sani sun yi magana

Tsige Sanusi II: Farfesa Auwal Yadudu da Sanata Shehu Sani sun yi magana

A daidai lokacin da ake cigaba da magana game da siyasar Kano. Shehu Sani ya cewa wani abu game da matakin gwamnatin jihar na tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II.

Shehu Sani ya yi hira da gidan talabijin na Channels TV inda ya bayyana matsayarsa karara da cewa matakin da gwamnatin Kano ta dauka ya sabawa kundin tsarin mulki.

Sanata Sani ya bayyana cewa an tsige Muhammadu Sanusi II ne saboda ya na fadawa gwamnati gaskiya, a cewarsa gwamnoni jihohi ba su son su ji wani ya fito ya soke su.

A game da mukaman da gwamnatin Kaduna ta ba tsohon Sarkin, Shehu Sani ya ce Nasir El-Rufai ya yi hakan ne domin nuna goyon baya ga Abokinsa Muhammadu Sanusi II.

A cewar Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna a Majalisar baya, da wannan nadin mukamai, Mai girma El-Rufai ya aika sako ga wadanda su ka tsige Sanusi II daga kan mulki.

KU KARANTA: Kashim ya jefa sako a cikin dabara ga ‘Yan siyasa bayan tsige Sanusi II

Tsige Sanusi II: Farfesa Auwal Yadudu da Sanata Shehu Sani sun yi magana
Shehu Sani ya na ganin akwai bukatar kawo dokokin da za su tsare rawanin Sarakuna
Asali: Original

Sai dai duk da yadda gwamnatin Kaduna ta ke jan tsohon Sarkin Kano da aka tunbuke, Sani ya na ganin cewa shi kansa gwamna El-Rufai ba zai iya jurewa sukar jama’a ba.

Sani ya ke cewa da ace shi ma Sarki ne, da sun samu sabani da gwamnan na sa a cikin sa’a 24. ‘Dan siyasar ya yi kira ga masu mulki su daina jin haushin masu sukarsu.

Da ya ke magana, Sani ya ce gwamnatin Kano ta dade ta na taso Sanusi II a gaba, har ma ya ba sa shawarar cewa ya kalubalancin tsigesa da tsare sa da ake yi a gaban kotu.

Auwal Yadudu wanda fitaccen Masani ne a harkar shari’a ya goyi bayan Sanata Shehu Sani, ya nuna cewa babu shakka tsare Sanusi II ya ci karo da kundin tsarin mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel