An cafke Lauyan da ya taimakawa Maras gaskiya ya tsere a Ebonyi

An cafke Lauyan da ya taimakawa Maras gaskiya ya tsere a Ebonyi

Wani Lauya mai suna Christopher Ajah, ya bayyana a gaban karamin kotun majistare inda ake zarginsa da hannu wajen garkuwa da mutane a jihar Ebonyi.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Southern City News, ana tuhumar Barista Christopher Ajah da taimakawa mai laifin satar mutane domin karbar kudin fansa.

Lauyan ya taimakawa wani Agbo Friday wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane wajen tserewa daga gidan yarin da ya ke tsare a Kudancin Najeriya.

Lauyan ‘Yan Sandan Najeriya, Mathias Eze, ya bayyana cewa ana zargin Ajah ya aikata wannan laifi ne a Ranar 5 ga Watan Fubrairun 2020 a Garin Abakaliki.

A Ranar Juma’a aka gabatar da shi a kotu da laifi guda na garkuwa da mutane. Idan aka same shi da laifi, Alkalin kotu zai iya yanke masa mummunan hukunci.

KU KARANTA: Adoke ya zabi zama a gidan maza a kan hannun EFCC

Barista Eze ya fadawa kotu cewa garkuwa da mutane ya sabawa sashe na 18(3) na dokokin laifuffuka da sha’anin tsaro a cikin kundin tsarin mulkin jihar Ekiti.

Masu kare wannan mutane har su bakwai, a karkashin shugaban kungiyar Lauyoyi na Abakili, Festus Nweke sun fadawa kotu cewa su na da ja a wannan shari’ar.

Festus Nweke ya bayyanawa Alkali cewa ba a nemi amincewar babban Lauyan gwamnatin jihar Ebonyi, kafin a shigo da wannan kara gaban kotun majistaren ba.

Masu shigar da kara sun nuna cewa ba su san cewa a dokar jihar, ana bukatar amincewar AGF kafin a gabatar da kara a kan garkuwa da mutane a gaban kotu ba.

Alkali mai shari’a, Nnenna Onuoha, ta bada belin wanda ake tuhuma bayan sauraron karar. Onuoha ta bukaci a bada N10, 000 kuma a samu wanda zai tsaya masa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel