Shehu Sani ya fadawa Hadimar El-Rufai ta je ta nemi Mijin aure a Tuwita

Shehu Sani ya fadawa Hadimar El-Rufai ta je ta nemi Mijin aure a Tuwita

Masu bibiyar shafin sada zumunta na Tuwita sun shaida wata ‘yar takaddama da ta kaure tsakanin Yaran gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma tsohon Sanatan jihar, Shehu Sani.

Wannan abu ya faru ne bayan an fatattako Tauraruwar nan Tacha daga shirin BBNaija wanda jama’a da dama su ke kallo. Sanatan ya nuna cewa zai koma bayan Merci bayan an yi waje da Tacha.

Fitaccen Sanatan ya yi wannan jawabi ne ta shafinsa na Tuwita inda yake cewa ya na fata ba za a zarge sa da yawan canza alkibla ba, saboda ganin a da, ya na cikin masu goyon bayan Khafi a shirin.

Jama’a su na ta surutun cewa an yi wa Sanatan ritaya daga siyasa, yayin da wasu ke mamakin yadda tsohon ‘dan majalisar dattawa ya buge da kallon wannan shiri, shi kuwa dai duk ya biye masu.

Yin maganar sa kenan, sai wata daga cikin masu ba gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shawara ta duro shafin Sanatan inda ta yi Allah-wadai kan yadda tsohon ‘dan majalisar ya koma kallon shirin BBNaija.

Maryam Abubakar ta ke fadawa Sanata Shehu Sani cewa: “Lallai! Abin da aka maida ka yi kenan? Tir.” Daruruwan mutane su ka maimata wannan sako, yayin da da-dama su ka nuna sakon ya burgesu.

KU KARANTA: Ina ganin yadda ‘Diya ta ke tafiya na san an yi mata fyade - Manomi

Sanatan ya yi wuf ya maidawa Hadimar gwamnan na jihar Kaduna martani inda ya ajiye batun siyasa a gefe guda, ya koma caccake ta. Sani ya fadawa Hadimar gwamnan ta je ta nemi Miji ta yi aure.

Shehu Sani yake cewa: “’Yar uwata, ki dage ki samu mijin aure, zaman gwauranci a irin wannan shekaru shi ne babbar masifa.” Inda ya ke nufin cewa kallon shirin na BBNaija da yake yi ba komai bane.

Hajiya Maryam Abubakar ba ta maidawa Sanatan na Kaduna ta tsakiya da ya rasa kujerarsa a zaben bana wani raddi ba illa cewa da ta yi: “Haha! Allah? Abin da kurum za ka iya kenan? An ji kunya.”

Mukhtar Garba Maigamo wanda shi ma ya na cikin Hadiman gwamnan da ke aiki tare da Abubakar, ya taya Abokiyar aikin ta sa sukar Sanatan, inda ya nuna cewa Takwararsa mutumiyar kirki ce.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel