Shari’ar Kano: Idan a na samun barazana za mu bar Kano – Alkali Shamaki

Shari’ar Kano: Idan a na samun barazana za mu bar Kano – Alkali Shamaki

A yayin da a ke cigaba da zaman shari’a a kan zaben gwamnan jihar Kano da a ka yi a bana, Alkali mai shari’a Halima Shamaki Muhammad ta yi barazanar maida sauraron karar zuwa Abuja.

Daily Trust ta rahoto Mai shari’a Halima Shamaki ta na kokawa da yadda mutane su ka fara kai hari a yanar gizo ga wasu daga cikin wanda su ka tsayawa hukumar INEC wajen shaida a kotun.

Kotun da ke sauraron korafin zaben gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Abba Kabir Yusuf na ganin idan a na yi wa wani mutum barazana, babu dalilin a cigaba da zama a Kano.

Babbar Alkalin wannan shari’a ta ce “Muddin akwai barazana ga ran wani don kurum ya zo gaban kotu ya bada shaida, gaskiya ba za mu cigaba da zama a nan mu na tunanin mu na tsare ba.”

A Laraba, 21 ga Watan Agusta, 2019 Halima Shamaki ta ke wannan gargadi ta na cewa: “Saboda haka da mu kama wannan hanya, idan ba haka ba don dole zan dauke zaman nan zuwa Abuja.

KU KARANTA: Zaben Kano: PDP ta tanadi shaidu fiye da 300 a gaban kotu

Alkalin da ke sauraron karar zaben ta yi wannan jawabi ne bayan wani kuka da Lauyan INEC ya kawo. Adedayo Adedeji ya fadawa kotu cewa a na yi wa wata shaidarsa Halima Sambo barazana.

Hajiya Halima Sambo Hassan ta yi aiki ne a matsayin Jami’ar zabe a cikin Garin Ungogo a Kano inda ta zo kotu ta bayyana abin da ya auku lokacin gudanar da zaben gwamna a farkon 2019.

Sai dai bayan ta bada shaidar ta, hotunanta sun fara yawo a kafafen sadarwa na zamani a na ci mata mutunci. Wannan ya sa a ka kawo kuka gaban kotu wanda Alkali ta nemi a binciki lamarin.

Lauyan PDP, Maliki Kuliya Umar, ya yi tir da wannan abu da ya faru. Ita kuwa babbar Mai shari’ar ta ce: “Idan har a ka sake mu ka koma Garin Abuja, sai dai ku bibiyi wannan shari’a a Rediyo”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel