Sojoji sun tafka ma 'yan Boko Haram mummunan asara a Abaganaram

Sojoji sun tafka ma 'yan Boko Haram mummunan asara a Abaganaram

- Sojojin Saman Najeriya (NAF) sun kai hari a sansanin 'yan ta'addan Boko Haram da ke kauyen Abaganaram

- Sojojin sunyi nasarar lalata gine-gine da dama tare da halaka wasu mayakan kungiyar a yayin da suke kokarin tserewa

- Rundunar Sojin ta ce ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai ta ga bayan dukkan 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin na Arewa maso Gabas

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta ce dakarun ta na sama (ATF) da ke atisayen Operation Lafiya Dole sun kai wani kwakwarar hari ga mafakar wasu mayakan Boko Haram da ke garin Abaganaram a Arewacin Borno cikin kokarin ta na kakkabe ragowar 'yan ta'ada da suka rage.

Kaakkain rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayar da sanarwar a ranar Asabar a Abuja inda ya ce an kai harin ne a ranar Juma'a.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga: Jami'an tsaro sun shiga farautar mabiya Shi'a a Abuja

"An kai harin ne ranar Juma'a 31 ga watan Mayu bayan bincike da bayyanan sirri na Sojojin Saman Najeriya (NAF) ya tabbatar da cewa 'yan ta'adda na zaune a wurin.

"Kazalika, Dakarun Sojin Saman sun aike da jiragen yaki biyu kirar Alpha Jet zuwa wurin inda su kayi nasarar yi musu ruwan bama-bamai a mafakan su guda uku wanda hakan ya yi sanadiyar lalata gine-ginen da ke sansanin tare da kashe wasu 'yan ta'adan," inji shi.

Daramola ya ce NAF ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai ta ga bayan dukkan 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel