Ko da Mai Martaba yayi laifi, Gwamna yayi tsauri – inji Sarkin Ningi

Ko da Mai Martaba yayi laifi, Gwamna yayi tsauri – inji Sarkin Ningi

Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, yayi magana a game da rikicin da ya barke tsakanin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da kuma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Sarki Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya ya bayyana cewa watakila Sarkin Kano yayi wasu kura-kurai a kan gadon mulki, sai dai a cewar sa, gwamnatin jihar Kano ta dauki mataki mai tsauri.

Mai martaba Sarkin na Ningi ya roki ‘yan siyasa da masu mulki su rika hakuri wajen hulɗa da masu sarautar gargajiya da su ka saba masu. Sarkin yace dole ayi kira ga duka ɓangarorin da ke rikici.

Tun farko Sarki Yunusa Danyaya yace abin da ya faru a jihar Kano ya bata masu rai, Sarkin yace ya zabi yayi magana a kan lamarin ne saboda girman shekarunsa da kuma dadewa da yayi a kan sarauta.

KU KARANTA: Manyan zabin da Ganduje ya ba Sarkin Kano

Ko da Mai Martaba yayi laifi, Gwamna yayi tsauri – inji Sarkin Ningi

Sarkin Ningi yayi magana bayan kirkiro sababbin Masarautu a Kano
Source: Facebook

Mai martaban yake cewa: “Ba mu ce Sarkin Kano bai yi wani laifi ba, amma bai kamata matakin da aka ɗauka ya shafi sauran mutanen kasar Kano da ba su ji ba, ba su kuma gani ba."

Sarkin yace: “A wuri na abin da ya faru a jihar ta Kano, abin kunya ne ainun kuma ba a taba tunanin haka zai faru ba. Tun daga lokacin mulkin mallaka har zuwa lokacin Sardauna ba a wargaza fadar Sarakuna kamar yanzu ba.”

“Daga lokacin da aka kacancana masarautar Kano, shikenan an rusa al’adar al’umma

Sarki na Ningi ya nemi a samu hadin kai tsakanin Mai martaba, da Gwamna da ‘yan majalisar dokokin domin ceto jihar Kano inda ya nemi a kafa wata majalisa a karkashin Sarkin Musulmi da za ta rika shiga tsakanin masu mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel