Harin Boko Haram ya yi sanadin rasuwa da jikkatan sojoji a Borno

Harin Boko Haram ya yi sanadin rasuwa da jikkatan sojoji a Borno

'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun sake kai hari a sansanin sojojin Najeriya da ke Borno inda suka kashe wasu, suka raunata wasu sannan wasu sojojin sun bata.

Sun kai harin ne a sansanin soji na 5 Brigade da 159 Task Force Battalion a ranar 19 ga watan Mayu a karamar hukumar Gubio misalin karfe 5:30 na yamma kamar yadda Premium Times ra ruwaito.

Sun kashe soja guda daya sun kuma jikatta sojoji uku kuma har yanzu akwai wasu sojoji shida da ba a gan su ba tun daren Talata da aka kai harin kamar yadda majiyar ta ce.

Sai dai sojojin sunyi kokarin dakile harin kafin 'yan ta'addan su tafka barna sosai inda suka kashe dan ta'ada guda daya tare da kwato bindigu.

DUBA WANNAN: Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

Harin Boko Haram ya yi sanadin rasuwa da jikkatan sojoji a Borno

Harin Boko Haram ya yi sanadin rasuwa da jikkatan sojoji a Borno
Source: UGC

Rundunar sojin Najeriya ba ta bayar da sanarwa a kan harin ba kuma Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Sagir Musa bai amsa wayar tarho dinsa ba yayin da aka kira shi da safiyar Laraba domin ji ta bakinsa.

Majiyar sojin da ya bayar da rahoton ya bukaci a sakayya sunansa saboda ba a bashi izinin fadawa kafafen yadda labarai harin ba.

Harin na zuwa ne kwanaki uku bayan rundunar sojin ta amince da bukatar mazauna Gubio ne sassauta dokar takaita zirga-zirga domin manoma su rika samun isashen lokacin aiki kafin komawa gida.

Manoman sunyi korafin cewa dokar takaita zirga-zirgan yana tilasta su baro gonakin su karfe 4 na yamma shi yasa suka bukaci a kara sassauta dokar zuwa karfe 5:30 na yamma kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Babu tabbas ko harin yana da alaka da sassauta dokar takaita zirga-zirgan da rundunar sojin tayi bisa bukatar mazauna garin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel