Al'ummar Gaya, Rano, Bichi da Karaye sunyi tururuwa zuwa majalisar Kano don nuna farin ciki

Al'ummar Gaya, Rano, Bichi da Karaye sunyi tururuwa zuwa majalisar Kano don nuna farin ciki

Al'ummar kananan hukumomin Gaya, Rano, Karaye da Bichi sun kai ziyara majalisar dokoki na jihar Kano domin nuna goyon bayan su ga matakin gwamnatin jihar na kirkirar sabbin masarautu a Kano.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba 8 ga watan Mayu ne majalisar dokoki na jihar ta amince da kudirin na kirkirar karin masarautu hudu a Gaya, Rano, Bichi da Karaye.

Masu goyon bayan kirkirar sabbin masarautun daga kananan hukumomin hudu sun isa majalisar ne karkashin jagorancin shugabanin kananan hukumomin su.

Saboda yawansu, majalisar ta bukaci a karo jami'an tsaro a harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

Kirkiran sabbin masarautu: Al'ummar Gaya, Rano, Bichi da Karaye sun ziyarci majalisar dokokin Kano
Kirkiran sabbin masarautu: Al'ummar Gaya, Rano, Bichi da Karaye sun ziyarci majalisar dokokin Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

A baya Legit.ng ta kawo muku cewa wani fitaccen masanin tarihi a Jami'ar Bayero ta Kano, Dokta Tijjani Naniya ya ce al'ummar jihar Kano ba za su amiince da yunkurin da gwamnatin jihar keyi na kokarin jefa masarautar Kano a cikin ruguntsimin siyasa ba.

Masanin ya yi wannan jawabin ne yayin mayar da martani a kan ikirarin da aka ce gwamnatin jihar za tayi na rage karfin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta hanyar kirkirar wasu masaurautu hudu a Karaye, Bichi, Rano da Gaya. .

Sai dai a wata hira da akayi da Mr Naniya a gidan rediyon Freedom a ranar Talata, ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda wasu 'yan siyasa ke yunkurin yin katsalandan cikin harkokin masarautar.

Ya ce yunkurin na kirkirar sabbin masarautu a Kano ba abu ne mai kyau ba kuma hakan zai sanya sauran kasashen duniya su mayar da Kano abin dariya.

Ya cigaba da cewa tarihi ya nuna cewa kimanin shekaru 800 da suka shude, masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye sun amince da yiwa masarautar Kano biyaya bayan an ci su da yaki a wannan lokacin.

"Tun wannan lokacin wadannan masarautun suna karkashin masarautar Kano ne. Kazalika, masarautar Kano ce ta nadi sarakunan da suka mulki wadannan masarautun. An zabi sarakunnan ne daga cikin wadanda suka yi jihadi a wannan lokacin.

"Tarihi ya nuna cewa masarautar Kano ba ta amince da katsalandan. Anyi yunkurin rage karfin masarautar a 1980 da 1981 amma hakan bai haifar da da mai idanu ba a wannan lokacin.

"Abin takaici ne yadda aka wofinta da kusan dukkan al'addun mu na gargajiya, sarakunan gargajiyan mu sune kadai abinda ya rage da 'yan siyasa ba su lalata ba. Ba zamu amince da hakan ba.

Ba za ta yiwu ba. "Masarautar Kano itace abinda ya rage da muke alfahari da ita saboda haka duk wata yunkuri da za ayi na kawo mata cikas ba zai yiwu ba," inji Naniya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel