An kama wani dattijo a Kano zai tafi Saudiyya da miyagun kwayoyi

An kama wani dattijo a Kano zai tafi Saudiyya da miyagun kwayoyi

Hukumar hana ta'ammuli da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wani dattijo mai shekaru 72, Mohammed Hamza da wani Kamisu Muhammad da haramtattun kwayoyi a filin tashi da saukan jirage na kasa da kasa ta Mallam Aminu Kano (MAKIA).

An damke dattijon ne yayin da ya ke kokarin shiga jirgi zuwa kasar Saudiyya.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a ranar Juma'a, Kwamandan NDLEA na MAKIA, Mr Ambrose Umoru ya ce an kamane Hamza wanda dan asalin kauyen Gwaranduma ne a karamar hukumar Daura a jihar Katsina a lokacin da ake bincikar kayayakin matafiya.

An kama wani dattijo a Kano zai tafi Saudiyya da miyagun kwayoyi
An kama wani dattijo a Kano zai tafi Saudiyya da miyagun kwayoyi
Asali: UGC

Sai dai dattijon ya shaidawa jami'an NDLEA cewa bai shi da masaniya a kan yadda akayi kwayoyin suka shiga jakarsa.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa matsalar garkuwa da mutane ya ki ci ya ki cinyewa - 'Yan sanda

"Mun gano cewa wasu ne da suka biya wa dattijon kudin jirgi zuwa kasar Saudiyya suka saka kwayoyin Tramadol a cikin jakar kayansa. Sun kawo shi Kano daga Katsina inda suka ajiye a Otel na kwanaki uku kuma a wannan lokacin ne suka saka kwayoyin jikin jakarsa ba tare da saninsa ba.

"A lokacin da jami'an mu suka gano muggan kwayoyin kuma ya fada mana inda ya fito. Ba tare da bata lokaci ba sai muka aike jami'an mu suka tsare Kamisu Mohammed.

"Kamar yadda bayannan mu suka nuna, an taba kama Mohammed da laifin saka muggan kwayoyi cikin jakkunan wasu mata biyu a baya. Sai dai a wancan lokacin matan tare suke aiki da Mohammed ba kamar dattijon nan da bai san hawa ba balle sauka," inji Umoru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel