Hisbah: Gwamnatin Jihar Kano za ta aurar da dubunnan Zaurawa

Hisbah: Gwamnatin Jihar Kano za ta aurar da dubunnan Zaurawa

- Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje zai aurar da Zaurawa da-dama a Kano

- Za a tantance wadanda za a aurar da su daga cikin asusun Gwamnati

- Daga cikin wadanda aka tantance an samu masu dauke da juna biyu

Hisbah: Gwamnatin Jihar Kano za ta aurar da dubunnan Zaurawa
Ana tantance matan da za a aurar da kudin Gwamnati a Kano
Asali: Twitter

Mun samu labari cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta aurar da dinbin Zaurawa a fadin jihar. Gwamnatin jihar za ta hada wasu Matan da su ka rabu da mazajen su ko kuma su ka rasu da mazaje na aure domin su samu sutura.

Hukumar ta Musulunci ta Hisbah ta tantance Mata har 8000 da za ayi wa aure daga cikin kudin gwamnati. Wani kwamiti ne aka nada mai dauke da mutane 23 domin yin wannan namijin aiki da zai rage neman mata a Kano.

KU KARANTA: Za mu ci gaba da yakin kamfe tun da an dakatar da zabe- Kwankwaso

Kamar yadda mu ka samu labari dazu, daga cikin wadannan matan da aka tantance an samu kusan 15 da ke dauke da cutar kanjamau mai garkuwar jiki da kuma wasu zaurawa fiye da 20 da ke rike da juna biyu bayan an yi gwaji.

An yi wannan gwaji ne domin tabbatar da halin lafiyar da wadannan mata su ke ciki kafin a nema masu mazaje. Bayan tantance mata 8000 da ke neman Iyali a fadin jihar, za a zabi 3, 000 ne rak da gwamnati za ta aurar daga Baitul Mali.

Za a zabo Matan ne daga cikin kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar Kano. Babban Limamin jihar watau Farfesa Sani Zaharaddeen ne aka nada ya jagoranci wannan gagarumin aiki da zai rage neman ‘yan matan banza a Kano.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel