'Yan Boko Haram sun sace dabobi da kayan abinci a harin da suka kai Maiduguri - NEMA

'Yan Boko Haram sun sace dabobi da kayan abinci a harin da suka kai Maiduguri - NEMA

- Mayakan Boko Haram sun sace shanu 200 da akuyoyi da raguna 300 a garin kauyen Bale-Shuwa da ke jihar Borno

- Yan ta'adan sun kai harin ne misalin karfe 7.30 na daren Asabar 10 ga watan Nuwamban shekarar 2018

- Hukumar bayar da agajin gagawa ta NEMA ta aika jami'anta domin taimakawa al'ummar da iftilai'n ya fadawa

Hukumar Bayar da Agajin Gagagwa na Kasa (NEMA) ta sanar da cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki kauyen Bale Shuwa da ke karamar hukumar Jere na jihar Borno a daren Asabar inda su ka sace shanu, raguna da akuyoyi.

Mai kula da ayyukan hukumar na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Alhaji Bashi Garga ne ya bayar da wannan sanarwar a Maiduguri.

'Yan Boko Haram sun sace dabobi da kayan abinci a harin da suka kai a Maiduguri - NEMA
'Yan Boko Haram sun sace dabobi da kayan abinci a harin da suka kai a Maiduguri - NEMA
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wani mai shekaru 95 da ya mutu ya dawo duniya

Garga ya ce: "Wadanda ake zargin yan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Bale-Shuwa da ke karamar hukumar Jere misalin karfe 7.30 na yammacin Asabar.

"An kashe wani mutum mai nakasa guda an kuma kone gidaje 65 kana an sace shanu 200, raguna da akuyoyi 300."

Garga ya kara da cewa tuni hukumar ta kai kayayakin taimako ga wadanda abin ya shafa a yayin da ana cigaba da naukan alkalluman abubuwan da akayi asara domin taimaka ma al'ummar da iftilai'in ya fadawa.

Kamfanin dillanci labarai NAN ta ruwaito cewar hankula sun kwanta kuma mutanen da suka gudu daga gidajensu sun fara dawowa bayan dakarun Sojojin Najeriya sun fattataki 'yan ta'adan da suka kai harin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164