2019: Takardun karatu na suna wajen Hukumar Sojin Najeriya - Al-Mustapha ya fadawa INEC

2019: Takardun karatu na suna wajen Hukumar Sojin Najeriya - Al-Mustapha ya fadawa INEC

- Dan takarar shugabancin kasa na PPN, Hamza Al-Mustapha shima ya gaza gabatar da takardun karatunsa ga INEC

- Kamar shugaba Buhari, Al-Mustapha shima ya ce takardun karatunsa na wajen Hukumar Sojin Najeriya

- Al-Mustapha ya bayyana cewar kotu ta umurci Hukumar Sojin ta mayar masa da takardun amma har yanzu ba ta mayar masa ba

Hamza Al-Mustapha, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Party of Nigeria (PPN) shima ya bayyana cewar takardun karatunsa suna wajen Hukumar Sojin Najeriya a yayin da ya mika fom din takararsa ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Dokar ya bukkaci dukkan masu tsayawa takarar kujeru a Najeriya su mika dukkan takardunsu na ga hukumar INEC cikin har da na karatu.

2019: Takardun karatu na suna wajen Hukumar Sojin Najeriya - Al-Mustapha
2019: Takardun karatu na suna wajen Hukumar Sojin Najeriya - Al-Mustapha
Asali: UGC

Sai dai Al-Mustapha, Manjo mai murabus ya fadawa INEC cewar takardun karatunsa na wajen hukumar sojin Najeriya.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

A yayin da ya ke mika sauran takardunsa, Al-Mustapha ya yi ikirarin cewar Hukumar Sojin Najeriya ta ki mika takardun karatunsa ga Hukumar INEC duk da cewar kotu ta umurci suyi hakan.

Al-Mustpha ya ce gwamnati ta kwashe shekaru 15 tana bincike a kansa amma daga baya kotun daukaka kara da wanke shi daga zargin da ake masa a ranar 12 na Yulin 2013.

"Gwamnati ta kwashe dukkan takardu na har ma da lambobin yabo da na samu a shekarar 1998.

"Na shigar da kara a babban kotun Legas a shekarar 2000 zuwa 2001 da kuma kotun tarayya da ke Legas a 2004 zuwa 2007 amma gwamnati ta ki biyaya ga umurnin kotu. inji Al-Mustapha.

Shima shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar Hukumar Sojin Najeriya ce ta rike masa takardun karatunsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164