Ronaldo Ya Sadaukar Da Otal Dinsa A Morocco Don Taimakon Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

Ronaldo Ya Sadaukar Da Otal Dinsa A Morocco Don Taimakon Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

  • Cristiano Ronaldo kamar yadda ya saba ya ba da gudumawar otal dinsa da ke kasar Morocco ga mutanen da abin ya shafa
  • Ronaldo ya ba da otal dinsa mai suna Pestana CR7 don zama masauki ga wadanda bala’in girgizar kasar ya shafa
  • Har ila yau, ‘yan wasan kwallon kafar kasar sun ba da gudumawar jini a kokarinsu na taimakawa wadanda su ke bukata

Marrakesh, Morocco – Shahararren dan kwallon kafar nan, Cristiano Ronaldo ya ba da gudumawar otal dinsa da ke Morocco don taimakawa mutane bayan girgizar kasa.

Ronaldo ya ba da otal dinsa mai suna Pestana CR7 saboda masauki ga wadanda iftila’in girgizar kasa ta shafa a kasar.

Ronaldo ya taimaka da otal dinsa a Morocco saboda girgizar kasa
Ronaldo Ya Ba Da Otal Dinsa a Morocco Don Taimakon Jama'a. Hoto: @AlNassrFC_EN @Africa_Archives.
Asali: Facebook

Meye Ronaldo ya taimaka da shi a Morocco?

Dan kwallon ya na da otal otal da yawa a Nahiyar Turai da kuma kasashen Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Zan taimake ku: Tinubu ya mika sakon jajantawa da karfafa gwiwa ga sarkin Moroko

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Al Jazeera ta tattaro cewa an samu girgizar kasa da ta yi ajalin mutane fiye da dubu daya tare da raunata 1,200 a kasar, Spotsbrief ta tattaro.

Shugabannin duniya sun nuna alhininsu kan wannan iftila’i da ta afkawa Morocco yayin da wasu kasashe su ka tura taimakonsu.

Akokarinsa na rage wa mutanen da abin ya shafa radadi ya ba da otal din dan ya zama mafaka ga wadanda abin ya shafa kamar yadda CristianoXtra ta wallafa a shafin Twitter.

Wane taimako 'yan kwallo su ka yi a Morocco?

A yayin ba da gudumawarsu a matsayin ‘yan kasa, dan wasan kwallon kafa na kasar, Achraf Hakimi da wasu daga cikin ‘yan kwallon kasar sun ba da gudumawar jini ga masu bukata.

Hakimi ya tura sakon ta’aziyya ga ‘yan kasar game da wannanr masifa da ta same su a daren Juma’a 8 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Tsadar Fetur: Yadda Abba Gida Gida Ya Yi Rabon Kayan Tallafi ga Mata da Manoma

Girgizar kasa ta hallaka mutum fiye da 1000 a Morocco

A wani labarin, girgizar kasa mai karfin gaske ta yi ajalin mutane fiye da dubu daya a birnin Marrakesh da ke kasar Morocco a daren jiya Juma’a 8 ga watan Satumba.

Ma’aikatar harkokin cikin gida a Morocco ta bayyana cewa wasu mutane kusan dubu daya sun samu raunuka a dalilin iftila’in.

Shugabannin duniya da dama sun nuna alhininsu tare da turan sakon jaje ga kasar Morocco bisa wannan bala’in.

Asali: Legit.ng

Online view pixel