'Dan Najeriya Ya Lashe Kyautar Gwarzon Ɗan Kwallon Afirka na 2024
- Ademola Lookman ya yi nasarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka na wannan shekara ta 2024
- Ɗan wasan tawagar Super Eagles da Atalanta yana ɗaya daga cikin ƴan kwallon da tauraruwarsu ke haskawa a nahiyar Turai
- Kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2024 za ta ci gaba da zama a Najeriya bayan Victor Osimhen ya lashe ta a bara watau 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika na shekarar 2024.
Wannan kyauta da ɗan wasan mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Atlanta ya lashe, ta sa ya zama ɗaya daga cikin ƴan kwallon mafi hazaƙa a duniya.
Fitaccen ɗan jaridar nan da ya shahara a ɓangaren ƙwallon ƙafa, Fabrizio Romano ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lookman ya zama gwarzon ɗan kwallon Afirka
Lookman ya lashe kyautar gwarzon dan wasan CAF na maza na 2024 a bikin da aka shirya ranar Litinin a birnin Marrakech na ƙasar Morocco.
Ya samu nasara ne bayan ya shige gaban abokan karawarsa Ronwen Williams, Simon Adingra, Achraf Hakimi da kuma Serhou Guirassy.
Yadda Lookman ya taka rawa a Atlanta da Najeriya
Tun farko an yi hasashen shi zai ci kyautar saboda bajintar da ya yi ya taimakawa Atalanta ta lashe kofin Europa kuma ya kai wasan karshe na AFCON 2024 da Najeriya.
"A hukumance, Ademola Lookman ya lashe kyautar Ballon d'or ta Afirka watau gwarzon ɗan kwallon ƙafa na nahiyar Afirka a 2024.
"Lookman ya samu wannan nasara kan abokan karawarsa, Ronwen Williams, Simon Adingra, Achraf Hakimi da kuma Serhou Guirassy."
- Fabrizio Romano.
Wannan nasara ta Lookman ta sa kyautar za ta ci gaba da zama a Najeriya bayan abokin wasansa a Super Eagles, Victor Osimhen ya lashe a bara watau 2023.
Rodri ya lashe Ballon d'Or 2024
A wani rahoton, kun ji cewa Rodri mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana 2024.
Ɗan wasan tsakiyar ya taka rawar gani a ƙungiyarsa da ke Ingila da kuma ƙasarsa ta Sifaniya a kakar wasan da ta shuɗe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng