NFF Ta Nada 'Dan Arewa a Matsayin Sabon Mai Horar da Tawagar Golden Eaglets Ta Nijeriya

NFF Ta Nada 'Dan Arewa a Matsayin Sabon Mai Horar da Tawagar Golden Eaglets Ta Nijeriya

  • A ranar Juma’a ne tawagar Golden Eaglets ta samu sabon koci, Manu Garba wanda ya jagoranci tawagarsa ta lashe kofin duniya na 2013
  • Wani bangare na aikin da ke jiran Garba shi ne shirya tawagar wajen buga gasar WAFU B ta 'yan kasa da shekara 17, da za a gudanar a Ghana
  • Garba wanda ya fito daga Arewa ya horar da manyan ‘yan wasan Najeriya kamar Kelechi Iheanacho, Taiwo Awoniyi, Isaac Success

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta nada tsohon zakaran gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, Manu Garba, a matsayin kocin kungiyar Golden Eaglets.

NFF ta nada sabon mai horar da tawagar Golden Eaglets
Garba ya taba jagorantar tawagar ta lashe kofin duniya na 'yan U17 a shekarar 2013. Hoto: @OgaNlaMedia
Asali: Twitter

'Yan wasan da Garba ya horar

Wani dan jarida mai daukar hoto na FIFA da CAF, Adepoju Tobi Samuel ne ya bayyana nadin Garba a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

A lokacin gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2013 a hadaddiyar daular Larabawa, Garba ya jagoranci 'yan wasan Golden Eaglets da suka lashe kofin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin 'yan wasan da suka saka burin Garba a lokacin ya zama gaskiya akwai Kelechi Iheanacho, Taiwo Awoniyi, Isaac Success, Musa Mohammed, Chidiebere Nwakali da Dele Alampasu.

Golden Eaglets ta daga kofin 2013

Tawagar ce ta kare a matsayi na biyu a gasar cin kofin Afrika na 'yan kasa da shekaru 17 da aka yi a Morocco bayan da Cote d'Ivoire ta doke su a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Sai dai kungiyar ta lallasa Mexico da ci 6-1 a wasansu na farko, inda suka yi kunnen doki (3-3) da Sweden, sannan ta lallasa Iraki da ci 5-0.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

A zagaye na 16, ta lallasa Iran da 4-1, ta ture Uruguay da 2-0 a wasan daf da na kusa da na karshe sannan ta lallasa Sweden da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe, kafin daga bisani ta lallasa Mexico da maki daya a wasan karshe don daga gasar.

Ana sa ran Garba zai jagoranci shirye-shiryen kungiyar na gasar WAFU B ta 'yan kasa da shekaru 17, da zai gudana a Ghana.

Ronaldo ya taya Musulmi murnar Sallah

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto Cristiano Ronaldo ya taya Musulmi murnar karamar Sallah, tare da yi masu fatan alkairi.

Ronaldo ya wallafa sakon barka da Sallah ne a shafinsa na X watau Twitter a ranar Laraba, yana sanye da fararen tufafin larabawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel