Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Isaac Promise ya rasu

Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Najeriya, Isaac Promise ya rasu

Tsohon kyaftin din Golden Eaglets da Flying Eagles, Isaac Promise ya rasu yana da shekaru 31 a duniya.

An sanar da rasuwarsa ne a shafin kungiyar kwallon kafa ta Austin Bold da ya ke bugawa wasa a turai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta suka fitar ya ce, "Austin Bold FC na cikin bakin ciki sakamakon rasuwar Promise Isaac wadda ya rasu a daren ranar Laraba yana da shekaru 31."

"Isaac ne dan kwallo na 7 da kungiyar ta saya a watan Augustan 2018 bayan ya shafe kakakin wasa 12 a Lig na kasar Turkiyya da na kasar Saudiyya."

DUBA WANNAN: Aisha ta aiko wa 'yan Najeriya sako, kakakinta ya kare ta

Shugaban Austin Bold, Bobby Epstein ya ce Isaac ya yada jiki ya fadi ne a harabar dakin motsa jiki kuma ba a zargin an shirya masa wani sharri ne.

"Babban asarar da kungiya za ta iya yi shine mutuwar dan wasan ta ba rashin yin nasara a wasa ba," inji Epstein.

"A madadin kamfanin BOLD, muna yi wa matarsa da yaransa da iyalansa ta'aziyya da fatar Alah ya bazu juriyar rashinsa."

Marigayin ne kyaftin din tawagar Najeriya da suka lashe azurfa a wasan Olypic na 2008 da aka yi a Beijing. Kazalika shine kyaftin din kungiyar kwallon Najeriya na kasa da shekaru 20 da suka lashe azurfa a 2005.

Promise ya bugawa kungiyoyi 7 kwallo a kasar Turkey inda ya buga wasanni sama da 350. Ya zirra kwallaye 77 a dukkanin wasannin da ya buga a yayin da ya ke raye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel