Taurarin Kwallon Kafa da Suka Mika Sakon Barka da Sallah Ga Mabiyansu

Taurarin Kwallon Kafa da Suka Mika Sakon Barka da Sallah Ga Mabiyansu

  • Wasu daga cikin taurarin kwallon kafa na duniya, sun aika da sakon barka da Sallah ga mabiyansu a shafukansu na soshiyal midiya
  • "Eid Mubarak! Ina yi muku fatan alheri, zaman lafiya da farin ciki a wannan rana ta musamman," in ji dan wasa Cristiano Ronaldo
  • Karim Benzema a cikin wani gajeren bidiyo ya ce, "Salam alaikum, Eid Mubarak zuwa gare ku baki daya, kuma Allah ya karbi idabunmu"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Riyadh, Kasar Saudiya - Shahararren dan wasan Portugal da ke buga kwallo a Al-Nassr Cristiano Ronaldo da dan wasan Al-Ittihad na Faransa Karim Benzema a ranar Laraba sun yiwa mabiyansu barka da Sallah.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a shingen binciken 'yan sanda, sun tafka babbar barna

Sakon barka da Sallah daga Ronaldo da Benzema ga mabiyansu
Taurarin kwallon kafa, Ronaldo da Benzema sun mika sakon barka da Sallah ga al'umar Musulmi. Hoto: @Cristiano, @Benzema
Asali: Twitter

Manyan 'yan wasan 'Saudi Pro League', sun mika gaisuwar fatan alheri ga mabiyansu na Saudiya da ma na duniya a ranar farko ta sallar Idi, bikin da aka fara a ranar Laraba.

Sakon barka da Sallah daga Ronaldo

Ronaldo ya wallafa a kan shafinsa na X cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Eid Mubarak! Ina yi muku fatan alheri, zaman lafiya da farin ciki a wannan rana ta musamman."

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan labarin, sakon dan wasan na Portugal, Ronaldo ya tattara fiye da 'likes' 800,000, 'retweets' 80,000 da martanin mutane 18,000.

Martanin mutane kan sakon Ronaldo

Wani mabiyin dan wasan mai suna Nungua ya rubuta:

“Barka da Idin karamar Sallah, tauraro na, ina kaunarka."

Yaseen ya ce:

"Ina sonka."

Sadaf, wata mace mai son Ronaldo, ta rubuta:

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

"Ina yi muku fatan alheri a bikin Sallah."

Wani mabiyi mai suna Hsnain ya rubuta:

“Kwarai, rana ce ta musamman. Mun gode, wannan sakon yana da tasiri a zukatan miliyoyin mabiyanka."

Sakon barka da Sallah daga Benzema

Bafaranshen, Benzema ya wallafa wani gajeren bidiyo a kan shafinsa na X yana mai cewa:

“Salam alaikum, Eid Mubarak zuwa gare ku baki daya, kuma Allah ya karbi idabunmu baki daya.”

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan labarin, sakon dan wasan na Al-Ittihad, Benzema ya tattara fiye da 'likes' 128,000, 'retweets' 12,000 da martanin mutane 2,300.

Martanin mutane kan sakon Benzema

“Barka da Sallah, Karim. Ka shirya karawa da Al-Hilal."

- In ji Ahmad.

Wani mabiyin ya ce:

"Eid Mubarak, ɗan'uwa."

Abdol Mohsen ya rubuta da Larabci:

“Allah ya karba daga gare ku da mu!”

Wani mabiyin Benzema, Ali, ya rubuta:

"Mafi kyawun mutumin da ya taɓa yi mana barka da bikin Sallah."

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Abubuwan da ake so Musulmi ya yi a ranar hawan Idi

Wani mai goyon bayan dan wasan da ake kira Abu Zaid ya yi martani da harshen Faransanci, yana mai cewa:

"Barka da Sallah, kuma kowace shekara ka kasance mai basira yayin karawa da abokan adawar ku."

An hana 'yan kwallo yin azumi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar kwallon kafa ta Faransa ta haramta wa 'yan wasanta yin azumin watan Ramadan.

Wannan mataki na kasar ya jawo wasu daga 'yan wasan sun hakura da buga wasa a tawagar kasar, a cewarsu, kwallon kafa ba za ta iya hana su bauta wa Allah ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel