Yaran Golden Eaglets sun doke ‘Yan kasar Hungary da ci 4-2 a U-17

Yaran Golden Eaglets sun doke ‘Yan kasar Hungary da ci 4-2 a U-17

- An tashi wasan Najeriya da kasar Hungary da ci 4-2 a gasar U-17

- Golden Eaglets sun taso daga baya har sau biyu sun doke Hungary

- Kyaftin din Golden Eaglets, Samson Tijani, ya zura kwallaye biyu

Wasan Najeriya da kasar Hungary ta kare da ci 4-2 cikin ban kaye a wasan farko da rukuni na biyu a gasar cin kofin Duniya. ‘Yan wasan da ke kasa da shekaru 17 ne su ke fafatawa a Brazil.

A Ranar Asabar, 26 ga Watan Oktoba, 2019, Golden Eaglets su ka kara da ‘Yan wasan kasar Hungary a filin wasan Olimpico Pedro Ludovico ke Brazil. Tun a minti na uku aka ci Najeriya.

Gyorgy Komaromi shi ne ya mamayi Najeriya ya zura masu kwallo daga fara wasa. Bayan minti uku dai kuma Najeriya ta kusa farkewa ta wani bugun firinkit da Ubani ya buga daga wajen raga.

KU KARANTA: Mawakin Najeriya Rarara ya bude filin wasan kwallon kafa

A minti na ashirin damar Golden Eaglet ta samu, bayan an doke Ubani a daf da gaban raga. Mai rike da kambun Najeriya, Samson Tijjani, ne ya doka bugun faniriti inda ya saida Golan Hungary.

A minti na 79 ne Najeriya ta farke wasan a sanadiyyar Usman Ibrahim. A cikin mintuna uku Najeriya ta ci kwallaye biyu. ‘Dan wasa Oluwatimilehin Adeniyi shi ne ya fara cin kwallo da kai.

A karshe kuma Kyaftin Tijjani ya ci kwallonsa na biyu wanda ya karawa Najeriya nasara. Idan dai Tawagar Golden Eaglets ta dage za ta iya kafa tarihi a Duniya ta ci kofin U-17 na shida a Duniya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng